✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara wasan kwallon kafa rukuni na biyu a Kano

A makon gobe ne za a fara gudanar da gasar kwallon kafa  ta ’yan rukuni na biyu reshen Jihar Kano ta shekarar 2017/2018, gasar da…

A makon gobe ne za a fara gudanar da gasar kwallon kafa  ta ’yan rukuni na biyu reshen Jihar Kano ta shekarar 2017/2018, gasar da ake sa ran fiye da kungiyoyin wasan kwallon kafa 160 ne za su fafata a cikinta.

Shugaban Hukumar  Qwallon Qafa ta Jihar Kano Alhaji Sharif Rabi’u Inuwa Ahlan ne ya sanar da haka a wajen taron fitar da jadawalin yadda gasar za ta gudana wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Qofar mata.

Alhaji Sharif Rabi’u Ahlan wanda kuma wakili ne a Hukumar Wasan Qwallon Qafa ta Qasa ya ce an shirya tsarin fitar da jadawalin a tsakanin wakilan kungiyoyin da za su buga gasar domin tabbatar da

gaskiya da adalci a tsakanin kungiyoyin da kuma rage yawan korafe-korafe da ake samu daga wasu kungoyioyin a kan yadda ake tsara gudanar da gasar a shekarun baya.

Haka kuma ya bayar da tabbacin cewar hukumarsa za ta sanya ido a kan yadda gasar za ta gudana, inda ya ce za a yi amfani da filayen wasanni na Gwagwarwa da Qofar Na’isa da kuma Jami’ar Bayero, domin samun kammaluwar gasar a kan lokaci.