✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara gasar Cin Kofin Gwamnan Kaduna

  Hukumar kwallon kafa ta Jihar Kaduna (FA) ta bayyana aniyarta na fara gudanar da gasar kwallon kafa na kofin gwamnanJjihar Kaduna da aka fi…

 

Hukumar kwallon kafa ta Jihar Kaduna (FA) ta bayyana aniyarta na fara gudanar da gasar kwallon kafa na kofin gwamnanJjihar Kaduna da aka fi sani da ‘Gobernor’s Cup’ na shekarar 2017 kafin karshen watan nan da muke ciki. 

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Kaduna Alhaji Shareeff Abdullahi kassim ne ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da Aminiya.

“Manufar shirya irin wadannan wasannin da sauransu shi ne zakulo zakakuran ’yan wasan da za su rika wakiltar jiha a gasannin cikin gida har zuwa matakin kasa baki daya. Zuwa yanzu mun sanar da Kwamishinan Matasa da Wasanni sannan mun aikewa da dukkanin kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna da su fara shirye-shiryen tunkarar wasannin da kuma sauran wasannin da hukumar ke shiryawa da suka hada da ZAFA da KAFA da kuma JAFA,” in ji shi.

Shugaban ya kuma bayyana godiyarsa ga dukkanin jama’ar Jihar Kaduna da irin goyon bayan da suka nunawa ’yan wasan jihar da suka halarci gasar kwallon kafa na ’yan kasa na jihohin Arewa maso Yamma na ’yan kasa da shekara 13 (U-13) da na ’yan kasa da shekara 15 (U-15) da aka kammala cikin watan da ya gabata a Jihar Kano inda ’yan wasan Jihar Kaduna suka zo na daya a matakin ’yan kasa da shekara 13 bayan sun doke takwararsu ta Jihar Jigawa da ci hudu da daya sannan  jihar ce ta zo ta biyu a gasar ’yan kasa da shekara 15 bayan kungiyar kwallon kafa ta Jihar Kano ta lallasa ta da ci 3-2 a wasan karshe.

Kazalika kungiyar kwallon kafa ta Dolphins da ke Zariya ce ta lashe kofin (NWL) na kasa baki daya wanda aka kammala a garin Ilori ta Jihar Kwara.