Gwamnatin Tarayya ta ce za ta daidaita albashin ma’aikata a hukumomi da ma’aikatunta, domin kawar da bambancin da ke tsakaninsu.
Ministar Kudi Zainab Ahmed, ta ce za a daidaita albashin ne ganin yadda ake biyan ma’aikatan wasu hukumomi albashi mai tsoka, takwarorinsu da matsayinsu daya a wasu ma’aikatu kuma ke karbar albashin da bai taka kara ya karya ba.
- An kama dan bindiga ya kai hari a masallaci
- Yadda aka kubutar da Daliban Afaka 27
- Juyin mulki: ‘Fadar Shugaban Kasa na cikin rudani’
“Gwamnati na so ne ta daidaita albashi a kowane mataki. Bai kama a samu tazara mai yawa tsakanin ma’aikata da matakinsu na aiki daya ba.
“Abin da muke son yi shi ne kawo daidaito da adalci wurin biyan tare da rage yawan kudaden da ake kashewa.
“Daidaita albashin zai sa ma’aikatan gwamnati su rika samun albashi da babu bambanci sosai a tsakaninsu,” kamar yadda ta bayyana.
Ministar ta shaida wa ‘Taron Tattaunawa kan Dokokin Kasa’ da Hukumar Yaki da Ayyukan Zamba (ICPC) ta gudanar a ranar Talata cewa, tuni Shugaba Buhari ya ba wa Kwamitin Albashi na Kasa umarnin fara aikin.