✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a bude makarantu ranar 5 ga watan Oktoba a Nasarawa

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce za a bude makarantun Firamare da na Sakandire daga ranar 5 ga watan Oktoba na bana. Kwamishinan Ilimi ta Jihar,…

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce za a bude makarantun Firamare da na Sakandire daga ranar 5 ga watan Oktoba na bana.

Kwamishinan Ilimi ta Jihar, Hajiya Fatu Sabo, ta bayyana hakan a ranar Juma’a yayin zanta wa da manema labarai a Lafia, babban birnin jihar.

Ta ce hukuncin hakan ya biyo bayan tattaunawar da ta yi da kwamitin da Gwamnatin Jihar ta kafa da ya kunshi dukkan masu ruwa da tsaki domin bijiro da ka’idodin bude makarantun cikin aminci.

Kwamishinan ta ce Ma’aikatar Ilimi a jihar ta dauki dukkanin matakan kariya gabanin bude makarantun.

A daya daga cikin matakan dakile yaduwar cutar Coronavirus, Gwamnatin Tarayya tun a watan Maris ta bada umarnin rufe kafatanin makarantu a duk fadin kasar.