✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a bude makarantu ranar 21 ga wata a Osun

Gwamnatin Jihar Osun ta sanar da sake bude makarantun jihar daga ranar 21 ga watan Satumba. To sai dai dole sai jihar ta tabbatar da…

Gwamnatin Jihar Osun ta sanar da sake bude makarantun jihar daga ranar 21 ga watan Satumba.

To sai dai dole sai jihar ta tabbatar da bin matakan kariyar da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta shimfida.

Ana sa ran da zarar makarantun suka koma za su kammala zangon karatu na uku na shekarar karatu ta 2019/2020.

“Bayan mun gudanar da bincike a makarantun jihar domin tabbatar da irin shiye-shiryen da suka yi na sake budewa, gwamnati ta amince ta sake bude makarantun ranar 21 ga watan Stumba daga hutun annobar COVID-19 domin kammala zango na uku na shekarar karatun 2019/2020 wanda ake sa ran karewarsa daga 30 ga watan Oktoban 2020,” inji Kwamishinar Ilimi da Wayar da Kai ta jihar, Funke Egbemode a cikin wata sanarwa.

Ta kara da cewa, “Domin maye gurbin abin da muka rasa saboda kullen COVID-19, sabon zangon karatun 2019/2020 zai fara daga 9 ga watan Nuwambar 2020.

“Saboda bukukuwan Kirsimeti, makarantu za su tafi wani kwarya-kwaryar hutu daga 24 ga watan Disamba zuwa hudu ga watan Janairun 2021 domin fara zangon karatu na daya da zai fara ranar 22 ga watan Janairun.

“Makarantun za su dawo domin fara zangon karatu na biyu daga 1 ga watan Fabrairu zuwa tara ga watan Afrilu, yayin da zangon karatu na uku zai fara daga 26 ga watan Afrilu zuwa 23 ga want Yuli.