Hukumar Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) da ke Kano, ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda wani likita a asibitin ya yi sanadiyyar wani jariri ya rasa hannunsa.
An bayyana cewa jaririn wanda aka haifa makon da ya gabata ya zo da wata matsala wacce ta bukaci yi masa gwaji ta hanyar daukar jininsa.
Sai dai rahotanni sun ce ana zargin likitan likitan ya bar wa jaririn igiyar a jikin hannunsa tsawon awa takwas, lamarin da ya janyo hannun jaririn ya rube.
Rahotanni sun kuma ce tsawon awannin da aka dauka, babu likitan da ya zo ya duba jaririn har sai lokacin da mahaifiyarsa ta je wurin da yake kwance (dakin yara) don shayar da shi.
A yanzu haka likitoci a asibitin suna ganin cewa dole ne sai an yanke hannun jaririn sakamakon rubewar da ya yi.
A cikin sanarwar da Shugabar Sashen Hulda da Jama’a ta Asibitin, Hajiya Hauwa Muhammad Abdullahi ta sanya wa hannu, ta ce Hukumar Asibitin ta girgiza da jin wannan mugun labari wanda a cewarta a shekaru 33 da kafuwar asibitin hakan bai taba faruwa ba.
Hajiya Hauwa ta ce Hukumar Asibitin tana jajanta wa iyayen wannan jariri bisa ga abin da ya faru.
A cewarta, a halin da ake ciki an mika wa kwamitin da yake bibiyar matsalolin badakala da sakacin aiki wato (Committee on Negligence of Duty) domin yin zuzzurfan bincike tare da daukar mataki a kan duk wanda yake da hannu a cikin wannan sakaci da ya faru.
Shugaban Asibitin, Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe, ya yi kira ga duk marasa lafiya ko ’yan uwansu da ba su gamsu da yadda ake kula da lafiyarsu ko ta ’yan uwansu ba, a asibitin, da su gaggauta sanar da Hukumar Asibitin ta hanyar jami’anta wadanda ake kira da Servicom Desk Officers.
Farfesa Sheshe ya kara da cewa ta hanyar mika korafi ne kawai hukumar asibitin za ta iya kamowa tare da hukunta masu laifi.
Ya kuma yi kira ga mahaifin wannan jariri da ya taimaka wajen isar da makamancin wannan korafi ga kwamitin binciken da Hukumar Asibitin ta kafa ko kuma Sashen Hulda da Jama’a na asibitin.