✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yusuf Buhari ya dawo daga jinya

A maraicen Larabar da ta gabata ne Yusuf Buhari ya dawo daga kasar Jamus, inda aka kai shi jinya kwanakin baya a sakamakon hadari da…

A maraicen Larabar da ta gabata ne Yusuf Buhari ya dawo daga kasar Jamus, inda aka kai shi jinya kwanakin baya a sakamakon hadari da ya yi da babur a Abuja.

Yusuf, wanda shi ne da namiji kacal ga Shugaba Muhammadu Buhari, ya samu tarba a filin jirgin Nnamdi Azikiwe, Abuja. Wadanda suka tarbe shi sun hada da karamin Ministan Lafiya, Dokta Osagie da Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello da wasu daga cikin ’yan uwansa.

A fadar gwamnati Aso Rock Abuja kuwa, Yusuf ya samu tarba daga mahaifinsa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mahaifiyarsa, A’isha Buhari da Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdurrahman Dambazau da ’yan uwa da abokan arziki.

Idan ba a mance ba, a watan Disamba da ya gabata, an kwantar da Yusuf a wani asibiti mai zaman kansa da ke unguwar Gwarimpa-Abuja, inda bayan ya samu sauki aka sallame shi, kafin daga bisani aka fitar da shi zuwa kasar Jamus.