✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunkurin tsige Olubadan cin mutuncin al’umma ne – Masarautar Ibadan

Masarautar Ibadan ta bayyana yunkurin da wasu masu rike da sarautun gargajiya suka yi na son tsige Olubadan daga sarautarsa, cewa cin fuska ne kuma…

Masarautar Ibadan ta bayyana yunkurin da wasu masu rike da sarautun gargajiya suka yi na son tsige Olubadan daga sarautarsa, cewa cin fuska ne kuma cin mutunci ne ga al’ummar Ibadan, domin kuwa ba su da ikon yin haka, kasancewar batun yana a gaban kotu a yanzu.

Kakakin fadar Olubadan, Mista Adeola Oloko ya ce: “Wannan wa’adi na kwanaki 21 da suke cewa sun bayar ga Olubadan, cin mutunci ne ga jama’ar Ibadan domin yanzu haka akwai kararraki 6 a gaban kotu a kan wannan al’amari, wanda daukar matakin nasu ya zama raini ne ga kotu. Kuma babu sunan Majalisar Sarakunan Ibadan a cikin dokar nadin sarautu ta Jihar Oyo. Saboda haka wannan haramtaccen sunan majalisa ne da doka ba ta san da shi ba.”

Batun daukaka darajar manyan fadawa da hakimai zuwa matsayin sarakuna a masarautar Ibadan da Gwamnan Jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi ya tabbatar da matsayin nasu watanni 3 da wucewa, wanda Olubadan na Ibadan Oba Saliu Adetunji ya ki amincewa da hakan, ya haifar da yunkurin tube shi (Olubadan) daga karaga.

Tun da farko, a Litinin da ta gabata ne wadannan sarakuna 21 suka ba Olubadan wa’adin kwanaki 21 da ya daina yin karan-tsaye a harkokin mulki na masarautar Ibadan. Sun ce za su goyi bayan tube shi daga karaga idan ya ki amincewa da yin amfani da gargadin nasu.

Da yake mayar da martani Olubadan ya ce, wa’adin kwanaki 21 da suke cewa sun bayar, abin dariya ne. Ya ce ba su isa su tube shi daga karaga ba, musamman saboda dokar nadin sarautu ta Jihar Oyo ba ta san da zaman wata majalisar sarakunan Ibadan mai suna Oba-in-Council ba.

daya daga cikin sarakunan, Oba Lekan Balogun shi ne ya yi wa ’yan jarida bayani a madadin majalisar sarakunan Ibadan mai suna Oba-in-Council. Dukkan sababbin sarakunan da Gwamna Ajimobi ya daukaka matsayinsu daga hakimai zuwa sarakuna sun halarci zauren taro na Mapo a Ibadan, a inda suka fito fili suka nuna wa duniya matsayinsu a kan wannan al’amari.

“Mun yanke shawarar bayar da wa’adin kwanaki 21 ga mai martaba Olubadan da ya canza salon mulkinsa domin ci gaban masarautar Ibadan. Idan ya ki yin aiki da bukatarmu a cikin wannan lokaci, to za mu mika shawarar goyon bayan tube shi daga karaga ga Gwamnan Jihar Oyo.” Inji Oba Balogun, wanda ya kara da cewa, tuni suka gano cewa Olubadan ne yake harzuka mutane da suke nuna kyama da bijire wa gwamnatin jihar.

Sun zargi Olubadan da gudanar da wasu muhimman abubuwa shi kadai, ba tare da sanar da majalisar tasu ba. Sun ce, daga ranar da Gwamna Abiola Ajimobi ya mika masu sandar sarauta da satifiket domin tabbatar da daukaka matsayinsu sai dangantaka tsakaninsu da Olubadan ta sukurkuce.

Olubadan ya nuna mamakin ganin tawagar fitattun mutane masana kamar manyan fadawansa da suka kai wani matsayi amma suka jefa kansu wajen daukar wani mataki a kan batun da yake gaban kotu. Ya ce: “Babu wani lokaci da fadar Olubadan ta ki karbarsu daga gudanar da abubuwa kamar yadda suka saba yi a baya. Duk da gujewa da kin halartar fadar, Olubadan ya ci gaba da gudanar da al’amuransa kamar yadda ya saba”

A binciken Aminiya, ta kalato Olubadan din yana cewa: “A tarihi, a baya babu wani Olubadan da manyan fadawansa suka taba bayar da shawarar tubewa daga karaga a masarautar Ibadan, wanda ba za a taba yin haka a zamanin mulki na ba.” Ya kara da cewa, yanzu haka akwai rubutattun wasiku 4 daga zuriyar bijirarrun manyan fadawan da suke bukatar fadar Olubadan ta maye gurbinsu da wasu mutane daban. Amma Olubadan ya ce ba zai yi haka ba, yana nan yana jiran komawarsu idan sun tube hulunan sarautar da suka sanya a kawunansu ba tare da masarautu ba.

Wutar wannan takaddama tana kara ruruwa ne a dalilin gabar siyasa a tsakanin Gwamna da ke kan gado, Sanata Abiola Ajimobi da tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rasheed Ladoja wanda yake tare da Olubadan a matsayin dan majalisar Sarkin Ibadan mai rike da sarautar Osi Olubadan.

A baya ma Gwamna Ajimobi ya yi ta zargin tsohon Gwamna Rasheed Ladoja da ruruta wutar wannan al’amari da ke neman tayar da zaune tsaye a masarautar Ibadan.