✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yayin da Jonathan ya kira taronsa

A yammacin ranar Litinin da ta gabata ce Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kaddamar da wakilan kwamitin kusan mutum 500 na fitattun ’yan Najeriya da…

A yammacin ranar Litinin da ta gabata ce Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kaddamar da wakilan kwamitin kusan mutum 500 na fitattun ’yan Najeriya da aka nada domin tattaunawa na wata uku kan al’amuran da suka shafi rayuwa da tattalin arziki don samar da matsayar da za su mika masa. Shawarwarin ne za a mika wa Majalisar Dokoki ta kasa wadda ta rantse ba za ta amince da kasafin Naira biliyan bakwai don gudanar da taron ba.
A zahiri daga baya Shugaba Jonathan ya karbi shawarar kiran taron kasa da masu da’awarta ke ganin za ta magance daukacin matsalolin Najeriya don dora ta a kan tubalin ci gaba. A ranar 1 ga Oktoban bara ne Shugaba ya karkata ga kiran taron kasar lamarin da ya ba ’yan boko, musamman masu kiran kansu ’yan kishin kasa da masu tunani irin nasu da suka dauki shekaru suna yada wannan da’awa. Manufar kiran taron ita ce a ba kasar nan damar duba ginshikan ci gaba da kasancewarta a matsayin kasa da yanke shawara kan tsarin gwamnatin da ta fi dacewa tare da magance batun da ake yawan maimaitawa na tsarin fedaraliyya da rage karfin gwamnatin tsakiya. Tarurrukan da aka yi a baya na tsarin mulki na Abacha da na sake fasalin siyasa na Obasanjo sun gaza cimma bukatun kusan kowa, ciki har da masu shirya su, Abacha ya gaza samun amincewar da ya nema, haka Obasanjo da ya kira taron don tazarce karo na uku. A yanzu kuma masu karfafa taron na Jonathan an fara kunyata su tun kafin fara shi, saboda ba taro ne mai cikakken iko ba, kuma ba na wakilan kabilu ba ne. Don haka duk da rashin sanin manufar kiran taron Jonathan, wannan jarida tana da yakinin matukar ba a jingine tsarin mulkin 1999 ko an kawar da shi ba, wannan taron ma zai wuce ba tare da tasirin kirki ba.
Ya kamata a tuna mahalarta taron ba wakilan jama’a ne ba, wakilan wadanda suka nada su ne, domin ba zabe ya tura su ba. Sannan yadda aka tsara taron ba wata doka da ta goyi bayansa don haka yana iya zama aikin baban giwa idan aka lura da tsarin mulki. Taron na iya zama wata mahada da ’yan boko za su gwagwaje a daidai lokacin da kasar nan take cikin halin ni’yasu. Mun amince da ra’ayoyin masu cewa duk abin da za a yi a taron a tabbatar ya zabi ajandarsa cikin natsuwa ta yadda za a kauce wa batutuwan da za su yi illa ga tsarin mulkin 1999 ko su kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro da zaman lumanar al’ummar kasa, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar zaben 2015.
Ya nuna cewa akwai yiwuwar taron ya zama na daga jijiyar wuya, kuma tabbas dakin taro na Cibiyar Shari’a ta kasa inda mahalarta taron za su barje guminsu na watanni zai ga maganganun takala da rarraba kai da barazana da ka iya kure hakurin shugabannin taron tare da kalilan din hobbasa don karfafa fahimtar juna da hakuri da juna da cimma matsayar da ake bukata a kasar da ke da matsaloli irin Najeriya.
Kamar kullum jaridar Aminiya  na maraba da duk wata dama ta tattaunawa mai amfani daga zababbun wakilan jama’a. Sai dai ba mu goyon bayan duk wani yunkuri da aka tsara domin tilasta ra’ayin marasa rinjaye a kan masu rinjaye kamar yadda dimokuradiyya ta nuna. Wannan ba wai saboda Najeriya ba ta fuskantar manyan kalubale ba ne. Domin ba a taba samun lokaci a cikin shekara 100 na Najeriya da take fuskantar barzana iri-iri kamar a yanzu ba, a bangaren tsaro da zamantakewarta da kayan inganta rayuwa da gazawar hukumomin kasa. A wurinmu mafita ita ce a inganta tsarin mulkin da muke da shi ta hanyar yi masa gyare-gyare, wanda abin takaici zababbun wakilanmu sun gaza yi. Kasa gyara tsarin mulkin 1999 ya karfafa wa masu tunanin taron kasa mai cikakken iko ne kawai zai iya magance dukkan matsalolin da suke tasowa.
Matsalar ita ce wannan tsari na yanzu ba za a kawar da shi da shawarar nadaddun wakilai da suka iya babatu da suka fito daga wasu ’yan kungiyoyi masu sha’awa ba. Kuma tsarin mulkin da muke aiki da shi bai lamunci a yi kuri’ar jin ra’ayin jama’a domin ba taron Jonathan damar shafe tanade-tanadensa ba. Wannan na nufin yayin da Shugaban kasa zai iya gudanar da taronsa, idan za a yi aiki da doka, shawarwarin kwamitin za su kasance masu bi ne ga abin da majalisar dokoki ta kasa ta yanke shawara a kai idan ta same shi. Kuma a yayin da zaben 2015 ke zuwa kasa da shekara daya, muna karfafa wa duk ’yan Najeriya gwiwa kan su hada kai su mayar da shi zaben da kasar nan take bukata, kuma su tabbatar sun zabi wakilai na kwarai da aikinsu na farko shi ne su gyara dukkan sassan tsarin mulki da a yanzu muke ganin suna kawo cikas ga ci gaban kasarmu a matsayin kasa. Wannan hanya ce za a samu matsaya ta kasa a kan zaben 2015 inda za a yi yaki sosai kan batutuwan da za su sanya ’yan majalisar dokokinmu su rika cancantar albashinsu, idan ba haka ba a rage shi zuwa yadda zai dace da hakikanin halin da muke ciki.