✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yayar tsohon Shugaban Kasa Yakubu Gowon ta rasu

Ita ce babbar yaya ga Yakubu Gowon

Babbar yaya ga tsohon Shugaban Najeriya zamanin mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, wato Maryamu Lami Dimka, ta rasu.

Lami wacce kuma yaya ce ga marigayi Kwamishinan ’Yan Sanda, SK Dimka ta rasu ne ranar Laraba.

Ta rasu ta bar ’ya’ya uku, ciki har da tsohuwar kwamishiniyar Zabe a jihohin Anambra da Bauchi Elizabeth Rimdans, da jikoki da dama.

Kafin rasuwarta dai ta rike mukamai daban-daban har zuwa jagorar kungiyoyi da dama, ciki har da Red Cross, da ta matasan mata Kiristoci, da ta masu fassara Baibul da sauran su.

Kazalika, ta kasance mai son harkokin Lambu da shuke-shuke, da kuma kida, har ma ta taba shiga sahun masu rera wakokin coci kafin tsufanta.

Tuni dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta bakin kakakinsa, Garba Shehu, ya mika ta’aziyyarsa ga tsohon Shugaban Najeriyar Yakubu Gowon da sauran iyalanta.