kungiyar Matasa Magoya Bayan dan Takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido mai suna Lamido Youth Mobilization of Nigeria, ta shirya taron addu’o’in neman samun nasara ga dan takarar nata a garin Jos babban birnin Jihar Filato.
Da yake yi wa wakilinmu bayani kan addu’o’in da suka shirya, Shugaban kungiyar na kasa kuma kusa a ayarin yakin neman zaben Sule Lamido, Abdulhadi Abdullahi Sani Cokali ya bayyana cewa sun shirya addu’o’in ne ganin cewa a duk ’yan takarar Shugaban kasar nan a karkashin Jam’iyyar PDP, babu wanda ya cancanci a ba shi takarar, kamar Alhaji Sule Lamido.
Ya ce don haka suka shirya addu’o’in bayan sun yi azumin kwana uku da saukar Alkur’ani kan Allah Ya bai wa dan takarar nasu nasara, a zaben da za a yi.
Ya ce Alhaji Sule Lamido shi ne ainihin dan PDP domin ba ya da sa’a a PDP kuma mutum ne tsayayye.