✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaya mutum zai yi idan wani na kusa da shi ya kamu da ciwon Hepatitis?

Amsa: To da yake matsalar ba ta gado ba ce, ba za a ce matsalar na yaduwa a tsatso ba, wato a ce dole ‘ya’ya…

Amsa: To da yake matsalar ba ta gado ba ce, ba za a ce matsalar na yaduwa a tsatso ba, wato a ce dole ‘ya’ya da jikoki sai sun yi. Amma da yake matsalar kwayar cuta ce da mutum kan iya sa wa matan da yake zaune da su, za a iya sa wa matar gida, ita kuma ta sa wa ‘ya’yanta idan ba a asibiti aka haihu ba. Abin da ya sa aka ce idan ba a asibiti ba shi ne da wuya ta sa wa ‘ya’yanta wannan ciwo a haihuwar asibiti saboda sai an mata gwajin wannan kwayar cuta da sauran wasu kafin ma ta haihun. Idan an ga irin wannan ciwo an san irin tanadin da za a mata da na jaririnta.

To idan ba a asibiti aka haihu ba kuma kwayar cuta ta samu ta shiga jikin jariri zai iya girma da ita bai sani ba, domin dama mun ce kwayar cutar za ta yi zamanta ne a hanta tana barci na tsawon shekaru. 

To wadanda aka ga irin wannan kwayar cuta a iyayensu suma dole ne su je su yi awon ciwon hepatitis su sani shin ko suna dauke da kwayar cutar ko kuma a’a. Idan suna dauke da ita su san cewa za su iya sa wa matansu su kuma su iya sa wa ‘ya’yansu. A hakikanin gaskiya zai wuya mutum ya auri maras wannan kwayar cuta a ce bai sa mata ba, ba kamar kwayar cutar kanjamau ba, wadda magungunan rage kaifinta suka wadata. Sai dai idan matar ta amshi riga-kafin kwayar cutar. Don haka aka fi so mutum da ya san yana dauke da wannan kwayar cuta ya fada wa yarinyar da yake so ya aura gaskiyar lafiyarsa tun ma kafin a je a yi gwaji. Idan ta ji ta gani haka take son sa shikenan sai ta yi allurar riga-kafi kashi uku, wato sau uku kafin a yi aure. Mu a likitance ma mun fi so mai wannan kwayar cuta ya nemi ‘yar uwarsa mai wannan kwayar cuta don allurar ba tabbas ne ta ba da kariya dari bisa dari ba. Yadda ake samun mata mai kwayar cutar kuwa shi ne sai an bi ta asibitin da aka yi gwajin aka fada wa mutum cewa yana da kwayar cutar. Ma’aikatan dakin jini za su iya taimakawa tare da hadin gwiwar bangaren kula da huldar jama’a na asibitin, domin hada irin wannan aure, kamar dai yadda ake wa masu dauke da kwaya mai karya garkuwar jiki.

Da gaske ne shan abubuwa masu daci kamar magungunan gargajiya za su iya illata hanta?

Daga Bello Tata, Kano

Amsa: E, da gaske ne wasu abubuwa masu daci guba ce da ka iya yi wa hanta lahani. Ai ba magungunan gargajiya ba, ko na nasara ma akwai maganin da yanzun nan idan aka afaa kamar kwaya ashirin a take hanta za ta mutu. Shi ya sa ake son masu sayar da magunguna na gargajiya su san ilmin tace magunguna ko su rika kaiwa tsangayoyin ilmin hada magunguna a jami’o’i ana tace musu gubarshi a kuma tsabtace shi.

Wasu masu maganin gargajiya ne ke ce mini wai ciwon daji ba ya son allura da zuwa asibiti. Shi ne nake tambaya a warware mini.

Daga Bashiru Shu’aibu

Amsa: Ai Malam Bashir ka san akwai bambanci tsakanin ilmi da ra’ayi. To ni dai ina ga ba zancen ilimi mai wannan magani ya maka ba, ra’ayinsa ya fada. Idan ana maganar ilimi ana kawo hujja, amma a ra’ayi ba a iya kawo wasu kwararan hujjoji. Don haka ka nemi Magana ta ilmi ba ta ra’ayi ba. Idan kana neman bayanai na ilmi akan ciwon daji ka nemi rubutun wannan shafi na shekarun baya a jarida ko ta hanyar intanet za ka ga batu na ilmin kimiyya.  

Da gaske ne shan lemo bayan an ci abinci zai iya sa saurin jin yunwa?

Daga Ibrahim Rabilu, Tsafe

Amsa: To ban san wane irin lemo kake nufi ba, na fata ne ko na kwalba. Ba dai sa saka saurin jin yunwa, sai dai su sa ciki da hanji saurin tsotse abinci da saukar da shi yadda ya kamata, musamman ga wadanda da sun ci abinci yakan zauna kabe-kabe a ciki ya ki wucewa.

Mene ne ke kawo habo? Cuta ce ita ma? Akwai alamun da mutum zai ji ya san cewa zai iya yin habo?

Daga Aminu Adamu Malam Madori

Amsa: Habo ba cuta ba ce, za ta iya zama alama dai ta wani ciwo, kamar ciwon tsinkewar jini ko daji ko hawan jini ko rashin bitamin mai tsayar da zubar jini wato bitamin na ajin K, da ma dai sauran irin wadannan cutuka da suka shafi tsinkewar jini. Amma a mafi yawan lokuta ba wata matsala ba ce da ta wuce bushewar hanci a yanayi na hunturu, wanda kan sa kananan jijiyoyin jini a cikin hanci bushewa su fashe. Wato kenan sai mutum ya fiya habo shi ne ciwo – a ce shi duk bayan ‘yan kwanaki sai ya yi, to sai ya je an duba shi an tantance wane ciwo ne ke sa masa habon.

Kusan kowace rana da yamma ta yi sai na ji jikina ya mutu kamar maras lafiya, amma da dare ya yi sai na ji ya warware. Ko hakan matsalar lafiya ce?

Daga Najibullah Salisu Dankama

Amsa: E, wannan ba alama bace ta ciwo, alama ce ta canjin agogon jiki, wanda ke nuni da cewa jikin na son a dan huta, abinda ake kira circadian rhythm a kimiyyance. Kusan kowa na da nasa lokacin jin kasala a rana. Wasu sai bayan azahar, wasu sai bayan la’asar, wasu da dare, wasu kalilan kuma kamar masu aikin dare, ta su kasalar da safe take tashi.

Shin wai ban da gyambon ciki na olsa mene ne kuma kan kawo zafin kirji?

Daga Bilya Shitu, Zamfara

Amsa: Akwai su Mallam Bilya. Manya daga ciki ma ai sune irinsu ciwon zuciya da bugun zuciya. Mutumin da kenan ya san ba shi da ciwon olsa idan ya ji kirji ko kahon zuci ya rike yana zafi to yana da kyau ya ziyarci asibiti. Idan abin ma yaki saki zai iya nuni da cewa sai an je asibitin ma cikin gaggawa.