A farkon watan nan ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin badi a zaman hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Kasa, kasafin ya fi ba da fifiko kan ayyukan raya kasa, bisa haka wakilanmu sun jiwo mana ra’ayoyin jama’a kan kasafin kudin:
Gaskiya akwai gyara a kasafin kudin –Al-Kassim
Daga Ahmad Ali, Kafanchan
Maganar gaskiya a kasafin kudin badi, akwai abubuwa masu sarkakiya da ban takaici. Misali, kudin da aka ware wa harkan ilimi, kiwon lafiya da noma, za ka gane anya mun yi shirin gyara kuwa a kan abubuwan da za su amfani talaka kai-tsaye?
Yawanci ana la’akari da jahiltar da daman ’yan Najeriya, musamman talakawa ke da shi game da kasafin kudi a Najeriya wanda duk shekara yana tsayawa ne kawai ga ’yan Majalisar Dokoki sai kuma ministoci da gwamnonin jihohi. Shi ya sa ba kasafai za ka ga talaka na maida hankalin wajen saurara ko bibiyar ayyukan kasafin kudin ba. Amma maganar gaskiya dole majalisa ta duba wannan kasafin kudi sannan ta yi gyare gyare a kai. Saboda bangaren ilimi da lafiya da noma an yi musu ba daidai ba.
Fatarmu a kan wannan sabon kasafin kudi ita ce talaka ya samu sassauci a kan halin da yake ciki a yanzu, na rashin aikin yi da rashin walwala kamar yadda taken yake nufi.
A gaskiyar magana akwai matsala – Sanata Shehu Sani
Daga Abbas Dalibi, Legas
Akwai matsala a kasafin kudin da Shugaba Buhari ya gabatar domin kasafin kudi ne da za a kara haraji, za a tsawwala wa talaka sannan akwai kashe kudi na garari sannan ba a fito da wata hanya da za a tallafa wa talaka ba. Don haka akwai matsaloli da yawa kunshe a cikin wannan kasafin kudi ya kuma rage ga ’yan majalisar su yi aiki a kai, su duba su gani su tantance inda ya kamata a yi gyara a gyara, ba wai da an kawo musu su rattaba hannu su ce komai ya yi daidai ba..
Kwalliya za ta biya kudin sabulu – Adamu Ya’u Ringim Kano
Daga Faruk Tahir Maigari
Bisa ga dukkan alamu kasafin kudin bana kwalliya za ta biya kudin sabulu domin an ware kudade masu yawa a bangaren samar da wutar lantarki da Ma’aikatar Ayyuka da gidaje da sufuri idan har gwamnati ta yi aiki da kasafin kudin badi to za a shiga Nes Labul.
Kasafin kudin badi akwai ci gaba sosai – Murtala Idris Alkajuriyyu
Daga Ahmed Ali, Kafanchan
Duk da dai ba a rasa fashin baki nan da can amma gaskiya kasafin badi ba abin da za mu ce sai Allah sam barka domin na badi, an kasafta tsarin manyan ayyuka za su ci Naira tiriliyan 4.88 inda ayyukan yau da kullum aka tsara za su lakume tiriliyan 2.14, hakan na nuna lallai muna matsawa gaba don manyan ayyuka sun ci wajen kashi 68 inda aka ba iwa na yau da kullum kashi 32 ba kamar gwamnatin baya ba.
Sannan abin sha’awa a kasafin shi ne yadda tattalin arzikinmu yake bunkasa don za a samu Naira tiriliyan 2.64 na kasafin ne daga man fetur da dangoginsa, sannan bangaren da yake daban, tiriliyan 3.7, sai bangaren da ba na mai ba tiriliyan 1.81 wato kusan kashi 85 za mu samu ne daga tattalin arzikin kasa.
Kasafin ya yi tagomashi a bangaren manufarsa don an tsara shi ne kan gama tsofaffin ayyuka kafin fara sababbi wadda shi ne abin da muka rasa.
Akwai ci gaba sosai – Desmond Elliot
Daga Abbas Dalibi, Legas
Akwai ci gaba sosai a kasafin kudin domin Juma’ar da za ta yi kyau daga Laraba ake ganewa. A wannan karon ba a samu wani jinkiri ba an gabatar da kasafin kudin a kan lokaci za a kuma kai karshensa a watan 12, maimakon yadda lamarin kan faru a baya inda ake haurawa har cikin watan 6 ko fin haka na wata sabuwar shekara. Sannan abin alfahari ne, sai dai fatata ita ce ’yan majalisa su bibiyi kasafin kudin duk inda ke bukatar gyara su duba a gyara domin ci gaban al’ummar kasa, domin su ’yan majalisar su ne muryar jama’a, suna zuwa yankunansu, suna kuma sane da korafe-korafen jama’arsu, na tabbata za su duba inda ake bukatar gyara su gyara.
Ba wani alfanu da zai haifar – Mustapha Garba Kiru
Daga Faruk Tahir Maigari
Kasafin kudin badi ba zai samar wa ’yan Najeriya wani ci gaban a-zo- a-gani ba. Domin gwamnati tana ware kudin tafiyar da gwamnati wanda yake fin na manyan ayyuka yawa. Idan ka duba kasafin kudi tun daga 2017 zuwa 2020 gwamnati ta fi fifita ayyukan tafiyar da gwamnati a kan manyan ayyuka. Don haka ba wani canji da za a samu.