Mai karatu ina fata ya zuwa wannan lokaci da kake karanta wannan makala an kawo karshen takaddamar da aka shiga tsakanin Gwamnan babban Bankin kasa Alhaji Sanusi Lamido Sanusi da Jami`an Kamfanin mai na kasa wato NNPC, ta bacewar wasu makudan kudade da suka kai Dalar Amurka20, kwatankwacin N3.25 tiriliyon (Biliyan sau dubu) na albarkatun danyen man feturda kasar nan ta sayar tsakanin watan Janairun 2012 zuwa watan Yulin 2013. A cikin wadancan watannin 19, kididdigar BabbanBankin ta tabbatar da cewa Kamfanin man ya sayar da danyenman fetur da dajararsa ta kai Dalar Amurka biliyan 67, amma Dalar Amurka biliyan 47, Kamfanin man na kasa ya iya sawa a cikin asusun gwamnatin tarayya da ke Babban Bankin kasar, ma`ana dai Dalar Amurka biliyan 20, ta yi batan dabo ko kasa ko sama, an nemesu kaura Wambai.
batan wadancan makudan kudade sun bayyana ga jama`ar kasa ne dama na duniya baki daya, bayan fitar takardar da Gwamnan Babban Bakin ya aika wa shugaban kasa Dokta Goodluk Jonathan a cikin watan Disamban bara, ya kuma bada shawarar ya kamata shugaban kasa ya sa a bincika. Ko kadan an ce bayyanar takardar a titi, bai yi wa Shugaba Jonathan dadi ba, al`amarin da ya kai matsayin da ake zargin Shugaba Jonathan, ya yi barazana ga Gwamnan Babban Bankin da lallai sai ya ajiye mukaminsa, barazanar da ya yi watsi da ita.
Kazalika, bayyanar waccan sama da fadin ce ta sanya a cikinwatan Disamban bara, Majalisar Dattawa ta umurci Kwamitintana harkokin kudi da lalle ya bincika mata, da aniyar ya gano shin gaskiya ne kudin da ake magana sun bacen kuwa ko dai karya ce kawai? A ranar Talatar makon jiya Kwamitin kudi na Majalisar Dattawan ya yi zamansa na biyu cikin sauraren ba`asin sassan biyu da suke takaddar bacewar kudin, Gwamnan Babban Bankin, ya dage akan cewar kudin da suke zargin sun bacen, yanzu bincikensu ya tabbatar musu da cewa sun kai Dalar Amurka biliyan 20, yayin da Manajin Daraktan rukunin Kamfanonin man fetur din na kasa Mista AndrewYakubu, shi kuma dagewa ya yi akan cewa ba sisin kwabon da ya bata, illah dai wai Gwamnan Babban Bankin ya jahilci yadda ake tafiyar da kashe kudin Kamfanin.
A zaman kariya, Mista Andrew Yakubu ya fada wa manema labarai bayan kammala zaman Kwamitin kudi na Majalisar Dattawan cewa ya yi, Kamfanin ya yi amfani da Dalar Amurka biliyan 8.49, wajen biyan kudin saukaka radadin janye tallafin man fetur, sannanya yi amfani da wasu kudin wajen gyara wasu bututun man da aka bata da sauran aikace-aikacen Kamfanin. Har sai da ta kai Mista Andrew, ya zargi Gwamnan Babban Bankin da cewa ya zama mai binciken kudi, wanda kuma ba aikinsa ba ne. Anan sai ya ce da rana daya Kamfaninsa ba ya shakkar a sa kwararrun masu bincike kudi da su binciki hada-hadar kudaden Kamfaninsa.
Duk da wannan kokarin kare kai da Manajin Daraktan rukunan Kamfanonin man fetur din ya yi, Gwamnan Babban Bankin, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi, ya kafe akan bayanan da ya bayar tun farko, yana mai kalubalantar Kamfanin man na kasa cewa iyakacin saninsa ya san cewa ikon da aka ba Kamfanin na biyan saukake radadin janye tallafin man fetur shi ne, ya shirya takardun biya ya mika wa kamfanin da ke kula da farashin man fetur ya biya, amma ba shi ya biya kai tsaye ba. Haka kuma Gwamnan Babban Bankin ya ce babu dalilin da zai sanya Kamfanin man zai ce yana biyan talalfin kanazir, alhali yana shigo da kowace litarsa akan N140, da yake cewa yana sayarwa akan N40, alhali a kasuwa ana sayar da litar kanazir din akan N170.
Mai karatu, wata daga cikin irin tabargazar da sama da fadin da ta bayyana ana tafkawa ke nan akan kudin man fetur din kasar nan bayan an sayar an karbi kudi, kasar da take ta daya a nahiyar Afirka akan arzikin man fetur, a duniya kuma tana rike da kambin zama ta tara a cikin kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, wato OPEC. Kar ka yi batun kiyasin da ake bayarwa na cewa a kullum kasar nan na asarar gangar danyen mai 150,000, ta hanyar sata da sama da fadi da ake, wanda akan wannan kiyasi ake kiyasta cewa kasar nan na asarar Dalar Amurka biliyan shida, duk shekara ta wannan hanya, baya ga sace-sace datayar da kayar baya irinta `yan kungiyar tsagerun matasan yankin Neja-Dalta, wadanda kan fasa bututun man fetur, ko dai da sunan sata ko don su kawo koma baya a cikin tattalin arzikin kasar nan.
Irin wadannan ta`addanci, su suka yi sanadiyar ya zuwa yanzu danyen man da ake hakowa, ya yi kasa daga ganga miliyan biyu da rabi zuwa miliyan biyu, wanda ba sai an fadi ba ya kara kawo raguwar kudin shigar kasar nan, tunda dama kusan kashi 90 cikin 100, na kudin shigar ana samunsu daga man fetur. Duk bayan wannan al`mundahana akan kudin man fetur din, mai karatu kar ka manta tsarin kasafin kudin gwamnatin taryya da ake duk shekarar inda akan ware sama da kashi 76 cikin 100, don ayyukan yau da kullum a kuma ware sama da 26 cikin 100, don gudanar da ayyukan raya kasa, wannan ma wata babbar hanya ce ta sace dukiyar kasar nan.
Duk da yawaitar wadandan sace-sace da jami`an gwamnati suka dukufa akan dukiyoyin al`umma. Sai dai wani abin farin ciki da karfafa gwiwa shi ne, irin wannan fallasawa da ake samu daga dai wadanda suke cikin gwamnatin, yana yi wa talakawan kasar nan manuniya cewa wata rana za a samu sauki matuka, koma a daina da yardar Allah. Allah Ka nuna manawannan lokaci.
Yaushe za mu ga karshen satar dukiyar kasa?
Mai karatu ina fata ya zuwa wannan lokaci da kake karanta wannan makala an kawo karshen takaddamar da aka shiga tsakanin Gwamnan babban Bankin kasa…