A yau Juma’a ne ake sa ran za a gudanar da jadawalin Gasar Cin Kofin duniya da zai gudana a Rasha a badi idan Allah Ya kaimu.
kasashe 32 ne suka haye gasar inda za a kasafta su rukuni-rukuni takwas inda kowane rukuni zai kushin kasashe hur-hudu. kasashe biyu ne daga kowane rukuni za su haye zagaye na biyu a yayin gasar.
Ana sa ran nuna jadawalin kai tsaye a fadin duniya a kafofin watsa labarai daban-daban ciki har da na yanar gizo da na talabijin da kuma gidajen rediyo irin su BBC da sauransu.
Za a kalli yadda jadawalin zai kaya ne da misalin karfe biyu na rana agogon Najeriya.
Idan za a tuna, kimanin makonni biyu kenan da Aminiya ta buga labarin yadda Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta jefa Najeriya a tukunya ta takwas amma a yanzu ne za ta san takamaiman kasashen da za ta fafata da su da kuma rukunin da za a jefa ta.
Sau hudu kenan Najeriya take halartar gasar cin kofin duniya. Ta halarci Gasar cin kofin duniya da aka yi a shekarar 1994 da 1998 da 2002 sai kuma wanda za a yi a yanzu a Rasha wato (Rasha 2018).
kasashen da suka haye gasar daga Afirka su ne Najeriya da Masar da Maroko da Tunisiya da kuma Senegal.
Za a gudanar da gasar ce a tsakanin ranakun 14 ga watan Yuni zuwa 15 ga watan Yulin 2018.