✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau za a yi gasar Gwarzon dan kwallon Afirka a Ghana

A yau ne ake sa ran za a gudanar da gasar Gwarzon dan kwallon Afirka a Ghana.  Wannan shi ne karo na uku da Ghana…

A yau ne ake sa ran za a gudanar da gasar Gwarzon dan kwallon Afirka a Ghana.  Wannan shi ne karo na uku da Ghana take daukar nauyin gudanar da wannan gasa. A karon farko wannan gasa za ta gudana ne a karkashin kulawar kamfanin AITEO maimakon kamfanin sadarwa na GLO.

’Yan kwallo uku ne za su fafata a wannan gasa da suka hada da Mohammed Salah dan asalin Masar da ke buga wa kulob din Liverpool na Ingila kwallo da Sadio Mane dan asalin Senegal da shi ma ke yi wa Liverpool kwallo da kuma Pierre-Emeric Aubameyang, dan asalin Gabon da ke buga wa kulob din Borussia Dortmund na Jamus kwallo.