✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau za a ci gaba da gasar La-liga ta Sifen, gobe kuma Gasar Firimiyar Ingila

A yau Juma’a ne za a ci gaba da gasar rukuni-rukuni ta kasar Sifen da aka fi sani da La-Liga bayan an tafi hutu yayin…

A yau Juma’a ne za a ci gaba da gasar rukuni-rukuni ta kasar Sifen da aka fi sani da La-Liga bayan an tafi hutu yayin da a gobe Asabar kuma za a ci gaba da gasar rukunin firimiyar Ingila.

A Sifen, a yau kulob din Leganes ne zai hadu da na Getafe da misalin karfe 8 na dare agogon Najeriya kuma wannan shi ne wasa karo na 3 tun lokacin da aka fara gasar.

A gobe Asabar kulob din Real Madrid ne zai hadu da na Lebante da misalin karfe daya na rana agogon Najeriya sai FC Barcelona za ta kece raini da Espanyol da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya.

A Ingila, a gobe Asabar kulob din Manchester City zai hadu da na Liberpool da misalin karfe 12 da rabi na rana agogon Najeriya sai Eberton ta hadu da Tottenham da misalin karfe 3 na rana a daidai lokacin da kulob din Arsenal zai kece raini da na AFC Bournemouth haka kuma akwai wasa a tsakanin Leicester City da Chelsea duk da karfe uku na rana.  Da karfe 5 da rabi ne kulob din Stoke City zai kece raini da na Manchester United.  Wannan shi ne wasa karo na hudu a Ingila tun bayan da aka fara gasar.

Jama’a da dama sun fi sha’awar kallon gasar firimiyar Ingila da kuma ta kasar Sifen da aka fi sani da La-Liga.