✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yarima Mathew ya zama sabon Attah Ighala

An nada Yarima Mathew Opaluwa Oguche a matsayin sabon Attah Ighala.

An zabi Alhjai Mathew Opaluwa Oguche a matsayin sabon sarkin Ighala (Attah Ighala).

Masarautar Ighala ta ayyana Alhaji Mathew a matsayin Attah Ighala ne bayan rasuwar Attah Ighala Igala, Michael Ameh Oboni II a 2020.

Sabon Attah Ighalan ya fito ne dan Cif Opaluwa Oguche Akpa ne na Gidan Sarautar Aju Ameacho na Masarautar.

Attah Ighalan ya yi karatunsa na firamare a makarantar St. Boniface a shekarar 1975, sai kuma sakandare a St. Peter’s College, wadda ya kammala a 1980, duk a garin Idah.

Ya yi digirinsa na farko da na biyu a fannin Gudanarwar Kasuwanci a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, tsakanin 1981 zuwa 1986.

A 1997 ya sake komawa ABU ya yi wani digiri na biyu kuma a fannin gudanarwar.

Alhaji Mathew tsohon ma’aikaci ne a Hukumar Zabe ta Kasa, inda ya yi aiki a sassa daban-daban, har ya kai matsayi Mataimakin Darakta.