✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yara uku sun mutu bayan kasa ta rufta masu a Kaduna

A jiya Laraba ne wasu yara uku suka rasa rayukansu bayan da kasa ta rufta masu a unguwar Karshen Kwalta da ke a Rigasa cikin…

A jiya Laraba ne wasu yara uku suka rasa rayukansu bayan da kasa ta rufta masu a unguwar Karshen Kwalta da ke a Rigasa cikin karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 3:30 na rana ‎ya jefa al’ummar unguwar cikin rudani.

Aminiya ta samu labarin cewa, biyu daga cikin yaran sun rasu ne nan take bayan duk kokarin da jama’a suka yi na fito da su ya citura.

Shi kuma daya daga cikinsu ya rasa ransa ne sa’oi kadan bayan an ceto shi daga cikin kasar da ta rufta.

Yara biyar abin ya shafa kuma dukkansu shekaransu sun fara ne daga 12 zuwa 16.

A yanzu haka biyu daga cikin su na jinya a wani asibiti inda suke karbar magani.

Babban Limamin masallacin juma’a na Karshen Kwalta malam Jamilu wanda shi ne ya sallace gawarwakin yaran ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya kuma bayyana cewa, yaran sun je hakar karfe ne a wajen da gwamnatin jihar ke yin wani gyarar gada a unguwar.

“An bayyana cewa sun je wajen ne domin hakar karfe a wajen da ake yin aikin gada. Suna cikin hakar ne kasa ta rufta masu. Daya daga cikin yaran mai Suna Zahradeen dan makwabci na ne,” in ji shi.

Ya kuma kara da cewa, kwanan su ne ya kare domin an rika korarsu daga wajen amma sai da suka koma.