✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yara miliyan 78 na fuskantar barazana saboda rashin tsaftataccen ruwan sha a Najeriya

Kaso daya cikin uku na yara a Najeriya ba sa samun tsaftattacen ruwan sha a gidajensu.

Asusun Tallafawa Yara Kanana na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce kimanin yara miliyan 78 suna fusantar hadarin kamuwa da cuttutukan da suke yaduwa ta ruwan sha guda uku.

Wannan bayyanin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Babban Darektan shirin WASH na UNICEF Dokta Jane Bevan wacce aka fitar a ranar Litinin.

“Kaso daya cikin uku na yara a Najeriya ba sa samun tsaftattacen ruwan sha a gidajensu, kana, kaso biyu cikin uku na yara ba su da makewayi.

“Ba kasafai ake mai da hankali wajen kula da tsaftar hannu ba inda kaso uku cikin hudu na yara kanan ba su da halin wanke hannayensu sakamakon rashin tsaftattacen ruwa da kuma sabulu a gidajensu.”

Bisa wannan dalili ne ya sanya Najeriya kasancewa daya daga cikin kasashe goma da suke fama da mutuwar yara a sakamakon cuttutukan da ake kamuwa da su a dalilin rashin wanke hannu kamar cututukan da suka danganci amai da gudawa, Bevan ta ce.

Ta kuma yi kira da a bai wa batun samar da tsaftattacen ruwan sha da zai dace da muhalli da bayyukan lafiyar jiki kulawa.

A cewarta, daukar wannan matakin ba kare lafiyar yaran kawai zai yi ba, amma zai taimaka wajen tabbatar da dorewar al’umma mai zuwa nan gaba.

Ta ce, “na tabbata muna bukatar inganta kulawar da muke bayarwa a wannan fanni ba tare da bata lokaci ba, har da samun kudade daga Asusun Muhalli na Duniya, inganta hanyoyin kare muhalli a shirin WASH da al’ummomin da ake gudanar da shirin.

Ta kara da cewa “a inganta tasiri da hanyoyin bin diddigi da kwarewa domin samar da ayyukan ruwan da tsafta, sannan a kaddamar da kudurin Majalisar Dinkin Duniya ta SDG6 tare da la’akari da shirin inganta tsarin.