✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar Marigayi Rashidi Yekini tana neman tayar da balli

Kimanin shekara hudu da mutuwar shahararren dan kwallon Najeriya Rashidi Yekini babbar ’yarsa Yemisi a makon jiya ta fito tana kiran da lallai a sake…

Kimanin shekara hudu da mutuwar shahararren dan kwallon Najeriya Rashidi Yekini babbar ’yarsa Yemisi a makon jiya ta fito tana kiran da lallai a sake yin bincike kan musababbin mutuwar mahaifinta Rashidi Yekini.
A hirar da ta yi da manema labarai a Legas  a ranar Larabar makon jiya, Yemisi wacce ke zaune a Ingila ta ce akwai bukatar gwamnati ta sake yin kwakkwaran bincike a kan musababbin mutuwar mahaifinta tun da bayanai sun tabbatar mahaifin nata kafin rasuwarsa yana cikin koshin lafiya ne, amma cikin kankanin lokaci ya shiga yin amai kuma aka garzaya da shi asibiti ,amma kafin a isa rai ya yi halinsa.  Ta ce wannan ya tabbatar musu cewa akwai yiwuwar an sanya wa marigayin guba ne a abinci kafin rasuwarsa.
“Muna so a gudanar da cikakken bincike kan dalilin mutuwar Babanmu, don na tambayi mahaifiyarmu ta ce ita ma ba ta san dalilin rasuwarsa ba.  Ta ce ta samu labarin ya rasu ne a wani waje da ’yan uwansa suka killace shi”.
Yemisi mai kimanin shekara 21 wacce yanzu haka take karatu a sashen koyar da yadda ake daukar wasan kwaikwayo (Cinematography)  a Jami’ar Leicester City da ke Ingila ta ce saboda rashin gamsuwa da yadda mahaifinsu ya rasu kimanin shekaru hudu da suka gabata ne ya sanya ta fara yin wannan kira don a bi musu kadi.
Yemisi ta ce a halin yanzu tana shirin mayar da katafaren gidan Rashidi Yekini da suka gada a Ibadan ne zuwa gidan adana kayayyakin tarihi (museum) inda za ta ajiye muhimman abubuwan da marigayin ya bari don a rika tunawa da shi.  Ta ce tana sa ran nan gaba kadan za ta shirya gasar kwallon kafa saboda tunawa da mahaifinta.  Ta ce za ta gayyato zaratan ’yan kwallo a ciki da wajen Najeriya musamman wadanda suka yi kwallo tare da mahaifinta a lokacin da yake raye don su kara a gasar.
Idan za a tuna, a kwanakin baya ne Lauyan iyalan marigayi Rashidi Yekini ya fito karara ya karyata labarin da wata kafar yada labarai a yanar gizo ta fitar inda ta nuna mahaifiyar Rashidi Yekini tana cikin mawuyacin hali.  Rahoton ya nuna tsohuwar tana sayar da koko da kosai ne a bakin titi don samun na kalaci saboda halin rayuwa.