✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanzu Gwamna Lamido ka san canjin sheka laifi ne?

Mai karatu idan dai kana da rai, to, kuwa za ka sha kallo, Ba don kome na fadi wannan karin magana ba, sai don irin…

Mai karatu idan dai kana da rai, to, kuwa za ka sha kallo, Ba don kome na fadi wannan karin magana ba, sai don irin yadda a cikin makon da ya gabata aka ruwaito Alhaji Sule Lamido Gwamnan Jihar Jigawa a yayin kaddamar da yakin neman zaben dan takarar neman mukamin gwamnan jihar a inuwar jam`iyyarsu ta PDP, Malam Aminu Ringim a garin Gwaram yana zargi wasu `yan siyasa da cewa marassa gaskiya da miyagun halaye ne, suka kewaye dan takarar neman shugabancin kasa na jam`iyyar APC Janar Muhammadu Buhari.

Ya fito karara ya zargi gwamnonin nan bakwai na jam`iyyarsu ta PDP da suka kafa sabuwar PDP, bisa ga zargin shugabanin uwar jam`iyyar tasu ta kasa da ita kanta gwamnatin tarayya ta PDP ba sa yi musu mulkin adalci. Gwamnonin da Gwamna Lamidon ya zarga su ne wadanda har da shi suka yi yunkurin kafa sabuwar PDP, wanda rashin samun hakan ta sa suka bar PDP, suka koma jam`iyyar adawa ta APC, su ne gwamnonin jihohin Kano, Dokta Rabi`u Kwankwaso da na Kwara, Alhaji Ahhmed Abdulfatah da na Sakkwato, Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako da na Ribas, Mista Rotimi Amaechi da Alhaji Murtala Nyako na Jihar Adamawa a wancan lokacin. Alhaji Lamido da Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Ma`azu Babangida, su suka ki canja sheka suka zauna cikin PDP.
Alal hali tarihin neman gyara a PDP din da gwamnonin suka fara ya dauko asali ne daga irin tarurrukan da gwamnoni uku, wato Gwamna Lamido da Gwamna Alhaji Wammako da gwamna Murtala Nyako suka fara ne, wadda daga bisani ya kai gwamnoni bakwai.
A wajen wancan yakin neman zabe, Alhaji Lamido ya fadi cewa “Kowane Kare da Doki, yanzu ya koma ya boye bayan Janar Buhari, `yan siyasa masu tarihin rashin gaskiya da miyagun halaye sun koma bayan Buhari, alhali a zabubbukan shekarun 2003 da 2007 da 2011, tare da su muka yaki Janar Buhari, amma yanzu ga shi da rana tsaka sun zama shahada`un Janar din.” “Idan har Buhari mutumin kirki ne, kamar yadda suka fadi, don me Buhari ya bari irin wadannan mutane suka kewaye shi,” inji Gwamna Lamido.
Ra`ayin Gwamna Lamido ne cewa abin kunya ne, mutanen da suka amfana, gagarumar amfana daga PDP, amma a yau suka zama manya-manyan makiyanta. Ya koka akan cewa a yau taken dake yawo a kasa shi ne CANJI, ta yadda duk wanda ya fadi haka shi ne wai ma`abucin CANJI. Anan sai ya bayyana cewa,“Mutane irinsu gwamna Kwankwaso da Alhaji Aliyu Wammako da Malam Nasir eL-Rufa`i da Alhaji Aminu Bello Masari da Alhaji Sabo Nakuku, duk jam`iyyar PDP ta yi su”, amma afadarsa wadannan `yan siyasa sun ci amanar mutanensu, don haka wai ba abinda ya can-can-cesu, da ya wuce jama`a su yi watsi da su a zabubbukan banan.
Abin sha`awa ne ka rinka jin wadannan kalamai daga masu mulki irinsu gwamna Lamido, gwamnan da a yau ba sai gobe ba, ba shi da tsara a cikin masu rike da wuyar yanka a cikin wannan mulkin demokradiyya, wato ma`ana kama daga mai rike da mikamin shugaban kasa zuwa na Kansila zababbe ko nadadde, kalilan ne tsaran gwamna Lamido, mafi yawansu kodaikanne ne koma `ya`ya. A dalilin haka ya sanya nike tsammanin gwamna Lamido ya fi duk wani dan siyasar da garansa yake garawa a yau sanin tarihin siyasar canjin sheka ta kasar nan wadda tun da aka fara harkokin siyasar janhuriya ta daya ashekarun 1960, ake fama da ita, wadda bata yi kamari ba sai a janhuriya ta biyu, 1979 zuwa 1983, lokacin da Alhaji Lamido, ya fara samun damar dana mikamin siyasa na Majalisar Wakilai a inuwar rusashshiyar jam`iiyyar PRP, ta marigayi Malam Aminu Kano.
Wadanda suka san abubuwan da aka yi a janhuriya ta biyu ko suka ji labari, sun san cewa wasu gwamnoni tara na jam`iyyun adawa na UPN da GNPP da PRP da NPP da `yan Majalisun Dokokinsu na tarayya da sunan ma`abuta ci gaba, sun hade kai,don ganin sun karbe mulki daga hannun jam`iyyar NPN ta shugaba Alhaji Shehu Shagari, cikin zabubbukan 1983.Jam`iyyar UPN ta madugun adawar wancan lokacin ce wato Cif Obafemi Awolowo, ya yin da NPP na tsohon shugaban kasar nan na farko ce wato Dokta Nmandi Azikwe, ya yin da GNPP ta Alhaji Waziri Ibrahim ce, ya yin da Malam Aminu Kano yake shugaban jam`iyyar PRP, ta su Alhaji Sule Lamido, wadda a lokacin ta kafa gwamnati a tsofaffin jahohin Kaduna da Kano.
A lokacin Cif Awolowo da Dokta Azikwe, suna da cikakken iko wajen jan linzamin gwamnoninsu da `yan Majalinsun Dokokinsu na kasa akan alkiblar da za su bi a zaman adawa da gwamnatin NPN, su kuwa su Malam Aminu Kano da Alhaji Waziri Ibrahim, babbar farraka suka samu tsakaninsu da gwamnoninsu da `yan Majalisun Dokoki na kasa, al`amarin da ya kai fagen aka raba gari suka kori gwamnoninsu da `yan Majalisun Dokokin da suka bi gwamnonin, haka ta sanya wasu daga cikinsu suka kafa bangare a jam`iyyunsu, wasu kuma sukai canjin sheka zuwa jam`iyyun NPP da GNPP, inda suka neman takarar mukamai daban-daban a inuwar jam`iyyun NPP da GNPP a zabubbukan 1983 din.
Ya zuwa yanzu ya kamata mai girma Lamido ya san cewa mutanen da ya zarga da sun zama butulu, bayan da jam`iyyar PDP ta mayar da su abin da suka zama a yau, ko kusa ba su zama batulu ba, idan aka yi la`akari da irin kimarsu da karbuwarsu a jihohinsu har ta ajiye `ya`yanta na asali ta ba su takara, kamar yadda aka yi a Sakkwato tsakanin Alhaji Muktari Shagari da Alhaji Wammako, da PDP din ta karbe takarar Shagari ta kuma nemi Alhaji Wammako yana ANPP, ya dawo cikinta ya yi mata takara. Me kuma Gwmna Lamido zai ce ga Gwamna Malam Isah Yuguda da PDP ta hana takara a shekarar 2007, ANPP, ta su Janar Buhari ta ba shi, ya kuma yi nasara ya barta?Haka labarin yiwa jam`iyya butulci yake ga gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi da ya ci zabe a inuwar jam`iyyar ANPP a shekarar 2007, ya barta ya koma PDP, ko kuma Gwamnan Jihar Kabbi Alhaji Sa`idu dakingari da ya ci zabe a shekarar 2007, a inuwar jam`iyyar ANPP, amma ya barta ya koma PDP, uwa uba tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da ya yi mataimakin shugaban kasa na shekaru takwas, amma ya bar PDP din. Kada ka yi batun canjin shekar da aka samu a wasu jihohin kudancin kasar nan. Ya kamata idan wasu dalilai na kashin kai, sun hana Gwamna Lamido barin PDP, duk da ba ya jin dadin zama cikinta, idan wasu sun bari bai kamata ya aibantasu da butulu ba, don kuwa kafin su yi wa jam`iyya butlci wasu sun yi.
Daga karshe ina taya Gwamna Lamido murna akan irin ayyukan a zo a ganin da ya yi wa jiharsu ta Jigawa cikin wa`adin mulkinsa, ayyukan da Allah Ya sa wadanda suka rigaye shi tunda aka kafa jihar a cikin watan Agustan 1991, sun kamata, to, kuwa da a yau ci gaban da ke jihar da ya fi haka. Amma batun wasu sun canja sheka ya kira su butulu bai taso ba a wannan lokacin.