✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yanomami: Kabilar da ke kone gawar danginsu su cinye

Suna ganin idan aka yi wa mamaci al’adar to zai yi nasara a kwanciyar kabari

Kabilar Yanomami wanda aka fi sani da Senema ko Yanam da aka fi samu a yankunan kasashen Brazil da Venezuela, a Kudancin Amurka, tana da wata al’ada mai ban mamaki ta kone duk wanda ya mutu a cikinta ta sarrafa ta cinye.

’Ya’yan wannan kabila ba su damu da abubuwan zamani ba, sun fi mai da hankali ga ci gaba da bin al’adunsu na gargajiya.

Sabanin yadda sauran kabilu ke binne mutum idan ya rasu, kabilar Yanomami ta bambanta na konewa ne ta ci naman matacce, duk lokacin da dan uwansu ya mutu ko wani da ke zaune a yankunansu.

Kabilar Yanomami tana da akidar cewa akwai bukatar a kare ran mutum ko bayan ya rasu, hakan kuma zai faru ne idan aka gasa ko kone gawarsa, kuma ’yan uwansa suka cinye naman.

Suna konewa ko gasa gawar sannan su bar kasusuwan kadai, sai su daka kasusuwan su koma gari su hada da tokar gawar.

Sukan yi amfani da garin da suka daka su hada wata miya, wadda suke amfani da ita wajen yin maganin rashin lafiya na gargajiya inda ’yan uwan mamacin ne za su yi amfani da ita.

Sun amince da cewa idan har aka yi wa mamaci wannan al’adar tasu zai yi kwanciyar kabari cikin nasara da zaman lafiya.

Ba kamar yadda aka saba bikin binne mamaci ba, su kabilar Yanomami ’yan asalin kabilun Indiyawan Daji, sun kasance suna kone gawar mamaci sannan su yi wa fuskarsu fenti daga tokar gawar mamacin.

Sukan yi waka tare da kuka don nuna alhininsu ga rasuwar dan uwansu.

A wani bangare na al’adar Yanomami kuma, idan wani makiyi ya yi kisa ko aka kashe wani dan yankin kabilar, mata ne kadai za su cinye naman mamacin da yin amfani da tokar gawar.

Daga bisani za iya ramuwa a kan wanda ya aikata kisan sannan za a yi bikin al’ada a daren aka yi kisan, yayin da za a yi ramuwar kisan a yankin da aka yi shi.