Haurobiyawa hakika mun ga tasku, musamman jin cewa, tsawon shekara manuniyar sama da aka yi ana ta gudun-loko da Jonatantin mulki da mu, babu abin da aka aiwatar illa watandar Hauro. Wannan watandar da aka yi da dukiyar kasar nan ita ta jefa Haurobiyawa cikin haure-haure da huragiya, har ta kai ga wasu na kokawa da jelen Baban-Burin-Huriyya a tsuntsun sama, inda ya karade wasu sassan duniya da kewayen nahiyoyi.
Batu na ingarman karfen karafa, ni ba mai lauye-lauyen dokoki ba ne, ballatana in ce zan bai wa wani kariya a gaban kulliya, amma dai na duba watsattsaken makalar Malam Ado, babanmu na kan kanya, wadda aka wallafa a wannan makon, inda ya yi tsokaci kan balaguron Baban-Burin-Huriyya. Wannan makala ta fayyace mana cewa, jelen Baban-Burin-Huriyya jelen jalauta jari ne.
Kuma ni ma ina da ra’ayi da fahimtar fasko al’amura, musamman ganin yadda jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge suka jirga mu tsawon shekara sili da manuniyar sama; kuma a cikin wadannan shekaru an shafe manuniyar sama ana yi mana wala-wala da damfarar damun fura, wai da sunan mulkin mulaka’u. Kowa a kasar nan na da labarin yadda ’yan watanda suka tatuke kasar nan. Jiga-jigan mai dan boto da sunansu ya fito kartara a wannan badakala, sun hada da: Baffan-Rawa da Samun-Bom- da-Sauki da Dokin-Fifsi da sauran miyagu masu magu-magu; ina yi musu addu’ar kada shugaban hana magu-magu a kasar nan ya rangwanta musu.
A daidai lokacin da nake yi muku watsattsaken darasin wannan mako, sai kawai na ji labarin cewa, wai Malam Namu-Duka da ke jan-gaban jaridar ’Yar-yau ko a ce “Wannan Rana,” in an murguda baki kamar an ci kilishi, an kan ga gilashi, ana ta yaren Ingilishi, musamman ga ma’abota ado da leshi, sai in ce muku ya haure da damin Hauro har malala gashin tunkiya manuniyar sama da babbban lauje, amma an ce ya arce. Lallai mai rera wakoki ratata ya yi batu, inda ya ce, “masu arcewa su tsere.”
’Yan makarantarmu idan har ba ku kakaba wa kurunku tagiyar Malam Mantau ba, za ku fasko yadda a cikin darusssanmu da suka gabata, na taba zargin cewa ko asusun Masanin Sisi-da-Sisi babu ko asi, shi ya sa har ya koka kan yadda ’yan Majalisar Haurobiya ke wawushe dami, ya kuma bukaci a zaftare yawan manyan ’yan kwadagon hukuma.
Takaddamar Masanin Sisi-da-Sisi da Mace-da-Zane game da wawushe damin Dalar Hauron Amurkawa har gashin balama karamin lauje da zagaye, wadanda aka zagaye da su, aka yi wa Haurobiyawa wa-ka-ci-ka-tashi! Tun daga wancan lokacin gama-garin al’umma suka fara ji a jikkunansu, musamman ’yan kwadago masu lalauben kadago da masu zaman dirshan a yankunan karkara da aka kusa yi musu kakara da kara.
Yau dai Mai martaba Masanin Sisi-da-Sisi Mai-duka ya bayyana hakikanin gaskiyarka, har ga shi an fito ana karin haske kan yadda jiga-jigan Gwamnatin Gudun-loko da Jona-tantin mulki suka yi watandar dukiyar kasar nan. Kuma ita kanta Madam In-Gwangwaje-in-Wala, ta bayyana yadda ta yi wala-wala da dimbin dukiyar da suka ce tsohon Shugaban Haurobiya mai dauke da harufffan Aa-baa-ca ya lakume, ashe su suka handame ta.
Allah Ya kara wa Babban Mutum Mai Rawani na Birnin Dabo ingancin uwar jiki, ya ci gaba da yin tonon silili ga su Malam Zalimu, wadanda suka shafe shekaru aru-aru suna zaluntarmu.
Lallai lokaci ya yi da Haurobiyawa za su taka wa ’yan watanda birki, kada mu sake ba su damar yi mana mulkin mulaka’u, tunda ko Turawa sun ba mu ’yanci da mulkin kai tun a shekara ta alif sili da manuniyar kasa da ta sama da zagaye, ba wani zagaye-zagaye.
Idan Baba Burin-Huriyya da jam’iyyar tsintsiyar kwakwa mai shara ta share batun ’yan watanda, ni dai babu ruwana. Sai dai jam’iyyar Baba ta sani mun kada musu kuri’un zabi-sonka ne don su yi mana magnain zogi da radadin ciwon kurungu, musamman a wannan lokaci da Haurobiyawa ke fama da talalar talauci, har wasu sun yi dan wuya kamar rakumi-rakumi zololo.
Masu koyon watsattsake da buda wagagewn littattafai a wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, kamata ya yi mu rera sananniyar wakar nan ta mu, ta ’yan watanda, ta yadda za mu taimaka wa su Samun-Bom-da-Sauki, su ji dadin zaman jarun.
“Yan makaran mu rera, sai ku ce: muna da rerawa:
Nanu guniya calka ko wahanda
Ginsamin nama watanda
Malam ya handame kaza
Kaza ta handame malam
Toyayyar masa a tanda
Busasshen kifi na banda
Fatar sa ta ganda
dingis-dingis dogaro da sanda
Tinkis-tinkis tafiya babu sanda
Mu yi yawo babu ganda
Mu yi maganin masu sanda
Da suke sace mana gyada
’yan mata a daina rangwada
Ko yawan wasan gada
Sai mun farmaki ’yan watanda,
Da suka jefa mu cikin kaka-ni-ka yi
Burin u su maishe mu bayi
Yau jikinsu ya fara laulayi
Wasu sun fara zawayi
Gararuma ta zama jimami
Bakinsu na hamami
Sun kasa zance bare watsattsaken alkalami
Da nufinsu sun samu a sanga
Sai ga shi ana kada musu ganga
Jarun dinsu an shinge shi da danga
’Yan dugwi–dugwi mu yi wasan langa
Babu sauran banga-banga
Kowa ya yi dubin mahanga
Ina ’ya’yan bayan katanga
Ga kwadago ku zo mu yi jinga
Miyagu masu magu-magu
Tuni an garkame su a lungu
An daure musu kugu
Suna ta shan bugu
Kada mu saurari masu far-far da ganda
Haurobiyawa tafiyar ku tazarce Uganda
’Yan watanda!
Haurobiyawa hakika mun ga tasku, musamman jin cewa, tsawon shekara manuniyar sama da aka yi ana ta gudun-loko da Jonatantin mulki da mu, babu abin…