✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan uwanmu 18 suka mutu a hatsarin ’yan Maulidi

Malam Saidu ya bayyana cewa tun bayan hatsarin, kullum sai an binne ƙarin waɗanda suka mutu

’Yan uwan waɗanda hatsarin mota ya rutsa da su a hanyar zuwa taron Maulidi a yankin Saminaka da ke Ƙaramar Hukumar Lere a Jihar Kaduna sun bayyana yadda kullum ake samun ƙaruwar mamata daga cikin matafiyan.

Ya zuwa ranar Laraba adadin waɗanda suka mutu ya karu zuwa 41, ciki har da 18 ’yan uwan juna, daga ƙauyen Kwandari, kamar yadda mazauna garin suka bayyana.

Wani mazaunin garin, Malam Saidu Dan Adabe Kwandari, ya bayyana cewa tun bayan hatsarin an ranar Lahdi, kullum sai an binne waɗanda suka mutu.

“A ranar Litinin, mun binne mutane biyu; a ranar Talata muka wasu biyu;  a ranar Laraba ma wasu biyu.

“Ya zuwa yanzu, an binne sama da mutane 41, tare da mutum ɗaya daga wani kauye mai maƙwabtaka da mu, Kundin Kurama,” in ji shi.

Hatsarin wanda ya afku a ranar Lahadin da ta gabata a daidai lokacin da mutanen ke tafiya garin Saminaka domin gudanar da bukukuwan Maulidi, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da dama.

Motar bas ɗin da suke ciki mai ɗauke da fasinjoji kusan 70 ta yi karo ne da wata tirela a kusa da garin Lere.

Malam Umar Abdullahi Kwandari, wanda kanensa ne ya tuƙa ba’a ɗin, ya bayyana cewa ’yan uwa 37 ne ke cikinta, inda 18 suka rasa rayukansu.

“Kanena, direban, da ɗansa duk sun mutu a hatsarin. Gaba ɗaya, ’yan uwa 18 muka rasa a hatsarin.

“Muna cikin bakin ciki sosai, amma muna godiya ga Allah akan komai,” in ji Umar.

Ya ce ’ya’yasa guda biyu kuma sun tsira da raunuka a hatsarin kuma ana yi musu magani.

Hakazalika, Saidu Dan Adabe Kwandari ya bayyana alhinin rashin ƙanwar mahaifinsa, Hajiya Halima Dodo, da ’yar yayansa mai shekara huɗu.

Ya kuma bayyana cewa abokinsa, Alhaji Munkailu, ya rasa matansa uku da ’ya’yansa biyu a hatsarin.

Biyu daga cikin ’ya’yan Malam Munkailu da suka tsira a halin yanzu suna kwance a asibiti.

Ya jaddada cewa irin wannan musiba, inda sama da mutane 40 suka rasa rayukansu a wani hatsari guda, bai taɓa faruwa a garinsu ba.

Ya bayyana cewa lamarin da ya jefa al’ummar garin gaba ɗaya cikin alhini.

Jami’an gwamnati sun ziyarci kauyen Kwandari domin jajantawa tare da bayar da tallafi ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa.