Wakilin Shiyyar Abiya ta Arewa a Majalisar Dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa ’yan takara 9 ne suke shirin janye wa Shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan domin tsayawa takarar Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar APC.
Kalu ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Asabar a Abuja, babban birnin tarayya.
- APC za ta fara tantance masu takarar gwamna da Majalisa
- Rikicin APC a Kano: Fadar Shugaban Kasa ta yi wa Ganduje da Shekarau kiranye
Uzor Kalu ya ce akwai daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa mai karfi a karkashin babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da yake shirin dawowa jam’iyyar APC nan ba da jimawa ba.
Duk da cewa Kalu bai bayyana sunan dan takarar ba, amma ya ce ya fasa yin takarar a jam’iyyar adawa ta PDP a matsayin wani yunkuri na goyawa Ahmed Lawan baya a jam’iyyar APC duba da jam’iyyar ta ki amincewa ta bayar da tikitin tsayawa takara ga dan takakar shugabanci daga Kudu Maso gabas.
Dan takarar dai ya bayyana goyon bayansa ga Lawan wanda ya fito daga Arewa maso Gabas.
A cewar Kalu “tsayawar takarar Lawan tamkar wata guguwa ce mai karfin gaske.
“Za a sasanta tsayar da dan takara gabanin gudanar da zaben fidda gwani.
“A yanzu da nake hira da ku kimanin ‘yan takarar shugaban kasa tara ne ke son janye aniyarsu ta tsayawa domin goyawa Ahmed Lawan baya a tsayawarsa takara da yake son yi ta shugaban kasa.
“Shin kuna ganin cewa wannan ba nasara ba ce gabanin zuwan zabe? Takarar Lawan za ta zama tamkar guguwa mai karfi.
“Na sha fadan dalilin da ya sa na janye aniyata ta takara kuma nasan cewa abu ne da ‘yan Najeriya suka riga suka sani.
Kazalika Kalu ya ce ba ya tsammanin Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta kara musu lokaci na gudanar da zaben fidda gwani kamar jam’iyyun siyasa suka nema .
Ya ce dama abu ne da aka riga aka sanar da dukkan jam’iyyun kamar yadda dokokin zabe suka tanadar.
“Ni ina goyon Hukumar INEC na tsayawa tsayin daka akan jadawalin da suka fitar, idan ba haka suka yi ba to za a yi ta dage wannan zabe. Kuma hakan ba daidai ba ne.
“Akwai bukatar Humukar Zabe ta Kasa mai zaman kanta da ta hukunta duk wata Jam’iyyar da ta kasa gudanar da zaben fida gwani a cikin wannan lokaci da aka ba da, saboda hakan ne kadai hanyar da za su san cewa sun dauki aikinsu da muhimmanci” Inji shi.