✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sandan Katsina sun ceto mutum 26 daga hannun masu garkuwa da su

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina tayi nasarar ceto mutum 26 daga hannun masu garkuwa da su a kauyen Dungun Ma’azu da ke cikin karamar hukumar…

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina tayi nasarar ceto mutum 26 daga hannun masu garkuwa da su a kauyen Dungun Ma’azu da ke cikin karamar hukumar Sabuwa.

‘Yan ta’addar sun je kauyen Badna-Buruku da ke karamar hukumar Chukun ta Jihar Kaduna a ranar 6 ga watan Janairu na 2020 akan babura 50, inda suka afkawa garin suka yi awon gaba da mutum 26, maza 18 mata 8.

Sannan suka shiga dajin Zamfara da su, daga bisani suka nemi a biya diyyar Naira milyan daya akan kowane mutum ko kuma su kashe su.

Wasu daga cikin wadanda aka ceto

Kamar yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan SP Gambo Isa, ya ce an kai wadannan mutane asibitin Ibrahim Commassie, domin duba lafiyar su kafin hada su da iyalan su.