✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun tilastawa korarren shugaban yankin Suleja fita daga ofis

Jami’an ‘yan sanda a yau Laraba sun tilastawa tsohon shugaban Karamar hukumar Suleja da ke jihar Neja, Malam Hussaini Ladan, wanda kotun daukaka karar jihar…

Jami’an ‘yan sanda a yau Laraba sun tilastawa tsohon shugaban Karamar hukumar Suleja da ke jihar Neja, Malam Hussaini Ladan, wanda kotun daukaka karar jihar ta kora fita daga ofis. Hakan na faruwa ne mintoci kalilan bayan ya samu damar shiga wurin.

Tun farko dai kotun ta ayyana wani tsohon shugaban Karamar hukumar Abdullahi Maje, da ya fafata da shi a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyarsu ta APC, amma bai yi nasara ba, a matsayin halattaccen dan takarar jam’iyyar.

Aminiya ta samu labarin cewa, a sakamakon hukuncin mataimakin Gwamnan jihar ya rantsar da Abdullahi Majen a ranar Litinin.

Sai dai a cikin hakan sai shi wanda kotun ta koran ya sake daukaka kara a babbar kotun daukaka kara ta tarayya a ranar Talata.

Ya samu shiga sakatariyar a yau Laraba a kan wannan dalilin, sai ‘yan sandan a karkashin jagorancin babban jami’insu na yankin Suleja suka tilasta masa fita daga wajen.

Izuwa lokacin aiko da wannan rahoton, ‘yan sandan na ci gaba da kasancewa a ciki da kuma waje na harabar sakatariyar a matsayin bada kariya, a yayin da ake dakon dawowar Majen daga Minna babban Birnin jihar, inda bayanai suka ce yana kan hanyar zuwa.