✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun saki ASD da Alkalin kotun shari’ah da ke tsare

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta saki dan Kasuwan nan Alhaji Sani Dauda wanda aka fisani da ASD tare da Alkalin Kotun Shari’a na Magajin…

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta saki dan Kasuwan nan Alhaji Sani Dauda wanda aka fisani da ASD tare da Alkalin Kotun Shari’a na Magajin Gari Murtala Nasir Almistry wadanda aka tsare su saboda aurar da ‘yar ASD da suka yi.

A ranar Litinin din nan da ta wuce ne ‘yan sanda suka kama ASD saboda aurar da ‘yarsa mai Suna Nusaiba da ya yi. Shi kuma Alkali Murtala Nasir Almistry, an tsare shi ne saboda wai shi ne ya daura auren.

Shima Yaron ASD din Shehu ASD har da shi aka rufesu amma kuma a ranar Laraban nan ne aka sallame su bayan sun kwana biyu a tsare.

Daya daga cikin ‘yan kusa da ASD wanda bai so a ambaci sunansa ya tabbatar da an sake su a Ranar Laraba” Eh, an sake su kuma sun koma gida,” in ji shi.

Shima daya daga cikin daliban Alkali Multala ya tabbatar da an sake shi” Kwarai an sake su duk a ranar Laraba,” in ji shi.

‎Ana zargin tsare mutanen uku na da alaka da rashin amincewa da aurar da tsohon mijin ita Nusaiba wanda aka ce yana da alaka da Sufetan Janar ‘Yan Sandan Najeriya ya yi ne. Domin ya nuna shi bai saketa ba.