✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

 ‘Yan sanda sun sake gurfanar da tsohon mai laifi a kotu

Wani tsohon mai laifi dan shekara 20 da ya haura gidan mutane tare da yin halin dan bera ya shiga hannu. Dan sanda mai shigar…

Wani tsohon mai laifi dan shekara 20 da ya haura gidan mutane tare da yin halin dan bera ya shiga hannu.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Idoko John, ya shaida wa kotu a Jihar Osun cewa matashin ya aikata laifin ne da yammacin ranar 24 ga watan Agusta a yankin Prime na Unguwar Ofatedo da ke Osogbo, babban birnin jihar.

ASP Idoko ya ce matashin ya tsallaka gidan wata mata, Oyeniyi Banke, inda ya lalata mata taga da kofofi wadanda darajarsu ta kai Naira dubu dari biyar.

Jami’in dan sandan matashin da ake tuhuma tsohon mai laifi ne an kuma sha kawo shi caji ofis.

Bayan sauraron karar, Alkali Opeyemi Badmus, ya ba da belin matashin a kan Naira dubu dari biyu tare da dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Satumban 2020.