Rundunar ’yan sanda a Jihar Edo ta karyata rade-radin da ke yaduwa cewa rikicin kabilanci ya barke a sakamakon kisan wani dan kabilar Ibo da wani Bahaushe ya yi bayan wata ’yar hatsaniya ta shiga tsakaninsu a titin Mission da ke unguwar New Benin a jihar.
A bayan nan ne dai shafukan sada zumunta suka cika da jita-jitar cewa rikicin kabilanci ya barke tsakanin Hausawa da ’yan kabilar Ibo a Jihar Edo, bayan wani Bahaushe ya kashe wani dan kabilar Ibo, wanda a sanadiyar haka han an kashe wasu karin mutum biyu.
- NAPTIP ta ceto mutum 10 da aka yi fataucinsu a Kano
- Buhari ya yi alhinin rasuwar Sarkin Kwatarkwashi
Bayanai sun ce wannan lamari da ya janyo tashin hankali a babban birnin jihar ya sanya mutane sun noke a matsugunansu saboda fargabar abin da ka iya zuwa ya komo.
Sai dai da yake magana da manema labarai, Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Chidi Nwazubor, ya ce har yanzu ba a san hakikanin wanda ya yi aika-aikakar ba domin kuwa babu wani bayani da aka samu dangane da sunansa, adireshinsa, kabilarsa ko kuma ’yan uwansa ba.
Ya ce “wani matashi wanda ba a kai ga sanin sunansa ba ballantana adireshinsa, kuma ana zargin cewa yana da tabin hankali, ya yi amfani da adda wajen raunata wani Mista Anthony Jibunor a gida mai lamba 116 a kan titin Mission da ke birnin Benin.
A cewarsa, biyo bayan kiran gaggawa da aka samu ne rundunar ta aika tawagar ’yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru, kuma suka riski wanda azal din ta auku a kansa ya yi shame-shame a kasa, yayin da wanda ya aikata lamarin ke hannun wasu fusatattun mutane da suka yi masa jina-jina a kokarinsu na huce takaici.
Nwazubor ya ce da kyar ’yan sandan suka kwato mutumin daga hannun fusatattun mutanen, kuma suka garzaya da duka wadanda lamarin ya shafa zuwa wani asibiti da ba a fayyace ba domin kula da lafiyarsu.
“Abun farin ciki a yanzu shi ne babu wanda ya mutu a cikinsu, duk wadanda lamarin ya rutsa da su suna samun kulawa a asibiti saboda haka jama’a su kwantar da hankalinsu.”
Kakakin ya ce Kwamishinan yan sandan jihar, CP Abutu Yaro, ya bukaci yan uwan duk wadanda abin ya shafa da sauran jama’a da su kwantar da hankalinsu, sannan su guji sa hannu a duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma.
CP Yaro ya bayar da tabbacin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta gurfanar da duk wani mai laifi.
Kazalika, ya gargadi masu goyo bayan daukan doka a hannunsu da su shiga taitayinsu ta hanyar mika wa hukuma duk wani wanda aka samu da laifi domin gudanar da bincike mai inganci.