✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kwato shanu 115 a hannun barayi a Filato

Hukumar ’Yan Sandan Jihar Filato ta bayyana cewa ta samu nasarar kwato shanu 115 dag0a hannun barayin shanu a jihar. Hukumar ta bayyana haka ne…

Hukumar ’Yan Sandan Jihar Filato ta bayyana cewa ta samu nasarar kwato shanu 115 dag0a hannun barayin shanu a jihar. Hukumar ta bayyana haka ne ta bakin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mista Austin Agbonlanhor a yayin da yake tattaunawa da ’yan jarida a hedikwatar rundunar da ke Jos a ranar Litinin da ta gabata.

Ya ce, hukumar ta samu nasarar kwato shanun ne sakamakon sahihin bayani da ta samu daga wani mutum mai suna Malam Abdullahi Yusuf da ke zaune a Karamar Hukumar Jos ta Kudu a jihar.

Ya ce, “Malam Yusuf ya bayyana cewa shanu 115 mallakar wani mai suna Ibrahim Suleiman dan shekara 33 sun bace a Sabon-Gidan Kanar lokacin da wadansu ’yan bindiga biyar suka tare shi sannan suka kwace shanun.

“Daga nan sai jami’anmu suka bazama, sannan muka sanar da jami’anmu da ke shingayen da ke kan hanyoyi a kan batun satar shanun, zage damtsen da jami’anmu suka yi ne ya sanya aka kwato shanun gaba dayansu, sai dai ’yan bindigar sun gudu da suka fahimci za a kama su,” inji shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa tuni rundunarsu ta mika shanun ga mai su, inda kuma ake ci gaba da bincike don gano wadanda ake zargi da sace shanun.