Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kame wasu jami’an Hukumar Kula da Ababen Hawa (KAROTA) na jihar, bisa zarginsu da lakada wa wani magidanci duka har suka karya shi.
Fitaccen dan jarida a Kano Salis Zango ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa kawo Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar CP Habu Sani ya umarci a mayar da binciken zuwa hedikwatar rundunar da ke Bompai.
Ya ce wata majiyar ‘yan sanda ta ce kame ‘yan Karotan ya fusata Hukumarsu har ta janye jami’anta daga hanyoyin jihar inda a baya suka saba gudanar da ayyukansu.
Sai dai Kakakin KAROTA, ya musanta hakan, inda ya ce babu tabbacin cewar ‘yan karota ne suka aikata wannan mummunan aiki, sai dai bincike zai bayyana gaskiyar lamarin.
A nasa bangaren Kakakin Rundunar’Yan Sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Kiywa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ana kan bincike a kai.
A ‘yan kwanakin nan ana samun tangarda a yanayin tafiyar da aikin jami’an KAROTA a Kano, domin ko a makon jiya an zargi wani jami’in Hukumar da galabaitar da wani matashi ta hanyar jona wa wata na’ura mai kashe jiki.
Da yawan mutane na kalubalantar hukumar ta KAROTA bisa yadda take wuce makadi da rawa a ayyukanta.
Wasumasana sharia na cewa hatta cin tarar kudi da karota ke yi a yanzu ya saba da doka, domin kotu ce kadai ke da ikon cin tarar mutane idan sun yi laifi, kuma kotuna suna hutun COVID-19, amma duk da hakan jami’an na ci gaba da cin tarar mutane.
Haka ma maganar dokar hana goyon babur da KAROTA ta ayyana shi ma masana sharia na cewa tamkar shiga sharo ne ba shanu.