Rundunar ’yan sanda a Legas ta yi nasarar kame wasu ’yan fashi da makami wadanda ake zargi da yin fashin tankar man fetur da ke makare da mai lita dubu 40.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan a Legas DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Asabar din da ta gabata ne jami’an rundunar suka kame wadanda ake zargin bayan bayanan sirri da suka samu, ya ce an kubutar da motar tankar Daf mai lambar 743 DN dauke da man fetur lita dubu 40, a kan hanyar Iyana da ke shiyyar Mil 2 a Legas, yayin da aka kubutar da direban babbar motar Muhammadu Mande, dan asalin jihar Kebbi da yaransa Lawalli Usman, dan garin Minna a Jihar Neja.
“Kana jami’an namu sun yi nasarar kame wadanda ake zargin masu suna Charles Obllomo mai shekaru 37 da ke zaune a unguwar Bara Ayetoro a yankin Apapa sai Osita Onyeka dan shekara 35 da ke zaune a unguwar Wasai a Orile, an kame su tare da karamar motarsu kirar Toyota Korolla mai launin ja wacce suka daure direban motar tare da yaransa a ciki, an kuma kama su da lambar mota da kakin soji,” in ji shi.
Ya ce, direban babbar motar Muhammadu Mande, ya shaida cewa an yi masu lodi a depot na Apapa inda suka dau hanya da zummar zuwa Kwantagora a jihar Neja inda za su sauke kayan, ya ce, suna nan tafe a yankin Mil 2 a Legas ne daidai kan hanyar da bata da kyau sai wasu mutum 4 cikin kayan sojin suka tsare su, inda suka tambaye su mai suke dauke da shi bayan sun fada masu sai suka umarce su su sauko su shiga karamar motar su kirar Toyota Korolla yayin da wasu mutum biyun da ’yan sandan suka kama suka ja babbar motar inda mutum 4 sanye da kayan sojin suka tuka karamar motar suna so a biya.
“Jami’an mu ne suka tsare su ko da suka fahimci basu da gaskiya sai suka kame mutum biyun da ke janye da tankar motarsu kuma suna sanye da kayan sojin sun yi musayar wuta da jami’an mu yayin da suka tsere da raunin bindiga a tare dasu, a irin haka ne suke daure direbobin suka jefar a daji, sun yi fashin man fetur da tankar, tun bayan zuwan sabon Kwamishinan ’yan sandan Legas Hakim Odumosun, yana sanya idanu sosai akan irin wannan,” in ji Bala Elkana.
Zuwa yanzu ana ci gaba da bincike wadanda ake zargin kafin daga bisani a gurfanar dasu a gaban kotu.