✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama jami’in tsaro da yi wa barayi safarar makamai

Rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar kama jami’in tsaro mai mukamin Sufuritanda na Hukumar Shige da Fice ta kasa  (National Immigration Service) a kan tuhumarsa…

Rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar kama jami’in tsaro mai mukamin Sufuritanda na Hukumar Shige da Fice ta kasa  (National Immigration Service) a kan tuhumarsa da yi wa barayin shanu safarar makamai a jihar Sakkwato.

An kama jami’in tsaron ne wanda ba a bayyana sunansa ba lokacin da aka kama wasu barayi kwanan nan.

Rahoton na bayyana cewa, wanda aka kaman na daya daga cikin wanda ke taimakawa barayin wajen addabar wata karamar hukuma da ke jihar.

Da wakilinmu ya tuntubi kakakin Hukumar Shige da Fice ta kasa  Bello Ahmad, bai ce komai sai dai ya ce jami’an ‘yan sanda na ci gaba da bincike.

Mukaddashin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Command, ASP Abdulkadir Datti,  ya ce a rahoton Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Sakkwato ta ce, an kashe sama da mutum 20 da tarwatsa sama da mutum 45,175 daga gidajen su, daga watan Yuli na 2018 zuwa yanzu a jihar.