Kwamishinan ’Yan sanda na jihar Kebbi, Garba Danjuma, ya ce rundunar ’Yan sandan jihar tayi nasarar kama barayin shanu tare da kwato shanu guda 36 daga hannun barayin a jihar Zamfara.
An yi nasarar kama barayin tare da kwato shanu a yankunan Zamfara da jihar Kebbi, sun samu nasarar ne lokacin da wasu mazauna kauyen Asarara su biyu Abubakar Juli da Alhaji Ardo, suka sanarwa jami’an ‘yan sandan bacewar shanun su 43.
Kwamishinan ya bayyanawa manema labarai hakan ne a Birnin Kebbi, inda ya ce sun yi nasarar kama wasu daga cikin barayin tare da shanun, yayin da wasu suka tsere.
Ya ce, sun yi nasarar kama wasu mutane guda biyu, Abubakar Umar da Attahiru Sani, mazauna garin Daki Takwas a karamar hukumar Gumi ta jihar Zamfara.
Ya kara da cewa, rundunar tana iya bakin kokarinta don ganin ta kama sauran barayin, inda ya kuma bayyana cewa suna aiki tukuru don ganin an kawo karshen sace-sacen shanu a yankunan jihar.