Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ’yan Najeriya su ne babbar matsalar kasar nan ba bambancin addini ko kabilanci da ake faman babatu a kansa ba.
Buhari ya fadi hakan ne yayin da ya karbi bakuncin ’yan kungiyar Muhammadu Buhari/Osinbajo (MBO) Dynamic Support Group, da ke goyon bayan shugaban da mataimakinsa, a ranar Laraba.
Cikin sanarwar da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar, Buhari ya ce “kanmu za mu zarga idan aka zo batun halin da Najeriya ke ciki, saboda irin rashin adalcin da muke yi a tsakanin junanmu da kuma wurin gudanar da alamura’.”
Sanarwar ta ce ’yan kungiyar sun kai wa Buhari ziyara ne don gabatar masa da kididdigar nasarorin da aka samu a tsawon shekara shida na mulkinsa.
Yayin karbar bakuncin yan kungiyar, Buhari ya yi waiwaye kan irin fadi tashin da ya shafe shekaru yana yi a gaban kotu don ganin an yi masa adalci a zabukan da yake da yakinin ya yi nasara a cikinsu.
A kan haka ne shugaban ya buga misali da cewa a zabukan 2003 da 2007 da kuma na 2011, duk mutanen da suka ki yi masa adalci ’yan kabilarsa ne kuma addini daya, inda ya ce wadanda suka tsaya masa kai da fata ’yan wata kabilar daban kuma masu akidar addini da ta bambanta da tasa.
“Matsalarmu ba kabilanci ko addini ba ne, mu ne matsalar kanmu,” in ji shugaban.
“Bayan na tsaya karo na uku a gaban Kotun Koli, na fito na yi magana ga wadanda suke wajen a lokacin inda na ce musu daga wannan shekara ta 2003, zan yi wata 30 ina zuwa kotu.
“Shugaba Kotun Kolin wanda ya saurari karar takarancin shugabancin kasar a lokacin, aji daya muka yi da shi a makarantar sakandare a Katsina. Mun shafe shekara shida a aji daya tare da Mai Shari’a Umaru Abdullahi.
“Jagoran lauyoyina, Cif Mike Ahamba, kirista ne kuma dan kabilar Ibo. A lokacin da babban alkalin kotun ya bukaci mu gabatar da kararmu, shaidana na farko ya bayyana.
“Ahamba ya dage sai an aika wasika zuwa ga Hukumar Zabe ta INEC, don ta gabatar da rijistar mazabun wasu jihohin, don tabbatar da cewa abin da suka sanar karya ne, tsara shi kawai aka yi.
“Bayan sun yanke hukunci, wani mutumin daban dan kabilar Ibo marigayi Mai Shari’a Nsofor, ya nemi jin ta bakin INEC kan wasikar da aka aika masa.
“Sai suka yi watsi da ita wanda kuma daga nan sai ya yanke hukuncin da ya banbanta da na sauran alkalan kuma wannan ya faru ne bayan shafe wata 27 kenan ana zuwa kotu.
“Daga nan sai muka garzaya Kotun koli. Wane ne babban mai shari’ar a lokacin? Bahaushe ne Bafulatani dan uwana, da ya fito daga Zariya.
“Mambobin tawagar sun shiga ciki sun yi kamar minti 30, sannan suka fito hutun gajeren lokacin. Amma bayan sun koma ba su fi minti 15 ba suka kori karar.
“A shekara 2007, wane ne babban mai shari’ar? Kutigi ne. Shi ma Musulmi ne daga Arewacin Najeriya inda shi ma bayan watanni takwas ya kori karar.
“Haka kuma ta sake kasancewa a shekarar 2011, saboda dagewa ta, Musdafa, wani Bafulatani kamar ni, daga Jihar Jigawa, shi ne babban mai shari’ar a lokacin kuma shi ma ya kori karar tawa.
“Duk na ba ku wannan labarin ne don na tabbatar muku da cewa matsalarmu ba ta kabilanci ko bambancin addini ba ce face mu ne matsalar kawunanmu.
“Na ki yarda na bayar da hadin kai kuma na yi kokarin komawa farar hula bayan abin da ya faru da ni a soji.
“Kuma kun sani cewa nima an min abin da na yi wa wadansu.
“A karshe ni ma an garkame ni a gidan kaso, inda na shafe shekara uku da ’yan kai, saboda haka Najeriya take.
“A yanzu ina fata malaman tarihi da masana za su adana wannan labari, domin kuwa wani ci gaba ne mai kyau a siyasance.
“Ya kamata jikokinmu da tattaba-kunnenmu su san fafutukar da aka yi, su fahimci cewa babu abin da muka samu cikin sauki kamar yadda wadansu mutane ke tunani.
“Ba wai don dimbin ma’adinan da yawan mutanen da muke da su ba, amma tabbas mun sha wahala sosai a wannan tafiyar.
“Na yi kokarin fadar wadannan abubuwa ne don ku hada kanku, ku yi amfani da damar da ta kuke da ita da kuma karfinku ba tare da na saka hannu ba.
“Babu wata godiya da zan yi da za ta wadatar kuma ba ni da bakin gode muku.
“Ina mika godiya ta a gareku kwarai da kuma sauran ’yan Najeriya saboda a shekarar, babu jihar da ban ziyarta ba cikin dukkan jihohin da ke kasar nan.
“Na yi haka ne saboda na sadaukar da kaina don bauta wa Najeriya da ’yan Najeriya saboda wannan soyayya ce da ta wuce misali.
“Haka kuma, ina yi wa Allah godiya ganin cewa cikin tsawon shekarun nan babu wanda zarge ni da cin hanci ba.
“Bugu da kari, na yi abubuwa tare da rike mukamai da dama a rayuwata daga Gwamna zuwa Ministan Man Fetur da Shugaban Kasar a zamanin mulkin soji da kuma Shugaban Kasa na farar hula har karo biyu.
“Ina godiya a gare ku kwarai da gaske duba da cewa babu wanda ya tilasta ku, amma kuka hada kanku, kuka yi amfani da dama da kuma karfinku a lokacinku.
“Ina mai tabbatar muku da cewa, tarihi zai yi muku adalci,” a cewar Buhari.