Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu, ya ce ’yan Najeriya na kewar mulkin jam’iyyar PDP na tsawon shekara 16 shi ya sa suke burin sake zabar ta a 2023.
Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da sashen Hausa na BBC.
- An sake bude makarantar da aka yi rikicin hijabi a Kwara
- Diyar malamar Kadpoly ta kubuta daga hannun masu garkuwa bayan shafe kwana 38
Ya bayyana haka ne bayan da jam’iyyar PDP ta bai wa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar tikitin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Atiku ya ce ya daura damarar fara yakin neman zabe domin tabbatar da karbe ragamar Najeriya a 2023 daga hannun jam’iyyar APC mai mulki.
A tattaunawarsa, Mu’azu Babangida Aliyu, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Tsofaffin Gwamnonin Jam’iyyar PDP, ya bayyana shirinsu na tunkarar zaben badi.
Ya ce dan takararsu ya shirya wa tunkarar babban zaben cikin shiri na musamman.
“Dan takararmu ya yi alkawarin kawo hadin kai da shawo kan matsalar tsaro, wanda shi ne ginshikin kowace gwamnati; kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
“Allah Ya taimake mu, ’yan shekara 16 nan da muka yi kan mulki sun shiga zukatan ’yan Najeriya har ta kai ga suna kewar mu saboda tabarbarewar da abubuwa suka yi a yanzu,” inji shi.
Yanzu haka ana tsimayin dan takarar da APC za ta tsaida a zaben shugaban kasa don karawa da Atiku da sauran ’yan takarar wasu jam’iyyun siyasa na Najeriya.