Matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya ya kai makura inda aka gano akalla mutum miliyan 20 ne a kasar suke mummunar dabi’ar.
Wani rahoto na Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ya nuna 6 a cikin kowane mutum 10 daga cikin mutum miliyan 20 da ke ta’ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya matasa ne, yawancinsu kuma dalibai ne a manyan makarantu.
- Majalisar Kano ta ba da shawarar cafke Muhuyi Magaji
- Buhari zai shafe mako biyu a Landan —Fadar Shugaban Kasa
Wani kwararre kan amfani da magunguna ba bisa ka’ida ba, James Ojomo, ya ce akasarin manyan birane kamar Kano, Kaduna, Abuja da Legs, su wayi gari a matsayin matattaran ’yan kwaya.
Yadda matsalar ta yi kamari
A kwanakin baya Aminiya ta kawo rahoton yadda hatta a cikin watan Ramadan matasa suka dukufa amfani da magungunan sanya kuzari da sauran miyagun kwayoyi.
Kakakin NDLEA na Kasa, Femi Babafemi, ya ce a ’yan watannin da suka wuce kadai Hukumar ta kama akalla mutum 400 da miyagun kwayoyi masu tarin yawa a sassa daban-daban na Nejeirya, ciki har da tashoshin jiragen sama.
Da yake bayani, Ojomo ya koka da cewa “Kasar ta dade ba ta mayar da hankali ba sosai wajen yakar matsalar, ana sakwa-sakwa da ita.
“Masu amfani da magunguna ba bisa ka’ida ba da masu fasa-kwaurinsu na cin karensu babu babbaka, har sun mayar da kasar wurin jibgewa, ba ma hanyar safara ba kadai.
A yayin da aka gano magunguna irin Tramadol da Kodin a matsayin wadanda aka fi amfani da su ba bisa ka’ida ba a Najeriya, Darakta-Janar ta Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce: “Tramadol da Kodin an tsara su a zaman 50mg da 100mg masu karfi, amma abin mamaki shi ne yadda kwayoyi masu 200mg da 225mg suka karade kasuwanni.”
Me ke kawo matsalar?
A jawabinta ga taron Ranar Yaki da Miyagun Kwayoyi ta Duniya ta 2020, Farfesa Adeyeye ta dora laifin yawaitar shan kwayoyin a kan rashin kula da magungunan da aka umarta.
Adeyeye ta ce sauran abubuwan da ke haifar da matsalar su ne tsabar son kudi na dillalan kwayoyin, rashin aikin yi, da kuma rashin bin doka.
Akwai kuma rashawa, rashin tsattsauran hukunci ga masu fatauci da dillalan kwayoyi, da kuma rashin cikakken tsaro a kan iyakokin kasar da ke ba wa masu fasa-kwaurin kwayoyi damar fataucinsu.
Dokta Obi Adagwu, masani ne a kan yaki da yaduwar miyagun kwayoyi, ya dora laifin matsalar a tsakanin matasan Najeriya a kan rashin dokokin hanawa da kuma rashin hukunta masu aikata laifin.
“Cibiyoyi nawa kasar take da su na gyara halin masu ta’ammali da miyagun kwayoyi? ’Yan kadan ne, amma yaya yanayin ingancinsu?’’
Shi ma Dokta Adagwu wanda masanin halayyar dan Adam ne, ya zargi gwamnati da rashin ba wa hukumomin da ke alhakin yaki da matsalar cikakken goyon bayan da suke bukata domin gudanar da ayyukansu.
Yadda za a yi wa tufkar hanci
A cewar Dokta Obi Adagwu, yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi aiki ne da ya kamata a faro daga cikin gidaje — a kan iyayen da ya kamata su zama abin koyi, amma ba sa lura da tarbiyyar ’ya’yansu.
“Wasu iyayen ba su ma san iya zurfin da ’ya’yansu suka yi wajen shan miyagun kwayoyi ba.
“Ya kamata kuma a kai yakin zuwa ofisoshin gwamnati, saboda akwai jami’an gwamnati da dama da ke ta’ammali da su,’’ inji shi.
Abin da gwamnati take yi
Da yake magana kan kokarin gwamnati wajen yakar mastalar, kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce sama da mutum 200 daga cikin mutum 400 da aka kama da laifukan suna fuskantar shari’a.
“Muna rokon kafafen yada labarai da daukacin ’yan Najeriya su taimaka mana da bayanai, mu kuma ba za mu gajiya ba wajen kawar da matsalar a Najeriya,” inji shi.
A nasa bangaren, James Ojomo ya ce, “Da sauye-sauyen da aka yi wa NDLEA, karkashin sabon shugabanta, Buba Marwa, Hukumar ta kara kaimi wajen yakar matsalar,’’ inji shi.
Ojomo ya ce abin da ya kamata shi ne ’yan Najeriya su rika fallasa dillalan kwaya wadanda ayyukansu ke neman lalata rayuwar matasan kasar.
Wasu ’yan Najeriya sun bayyana cewa a tsawon lokaci, gwamnatocin kasar sun yi kokari wurin farfado da martabarta ta fuskar yaki da safarar kwayoyi.
A cewarsu, gwamnatocin sun ba da muhimmaci kan hukumoin tsaro da kuma murkushe dillalai, wanda ya taimaka wajen kamawa da kuma daure masu laifin da dama.
Tsugune ba ta kare ba
Amma wasu kwararru na ganin cewa, duk da wadannan matakai da aka dauka, ba sa samu raguwar ta’ammali da miyagun kwayoyi yadda ya kamata ba.
Suna ganin sabon yunkurin NDLEA da goyon bayan da hukumar take samu daga Gwamnatin Tarayya za su taimaka gaya wajen saurin samun nasara a yakin da ake yi da matsalar.
Sun ba da shawarar a karfafi dokokin kasar na yaki da matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Daraktan Cibiyar Bincike kan Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi, Farfesa Isiodore Obot, ya ce Najeriya ta gaza a yakin da take yi da mastalar, idan aka yi kwatanta da yawan matasan da suka rungumi mummunar dabi’ar.
Da yake jawabi a taron wayar da kan ’yan jarida kan shan magunguna ba bisa ka’ida ba a Abuja, Farfesa Obot ya ce shekaru da dama bayan haramta amfani da miyagun kwayoyi a kasar, amma har yanzu haka ba ta cimma ruwa ba.
Ina mafita?
A cewar Shugabar NAFDAC, hanya daya tilo ta magance matsalar ita ce gwamnati ta samar tare da aiwatar da Tsarin Bayar da Magunguna ta Kasa.
Adeyeye ta yi kira ga bangarorin gwamnati uku da kada su gajiya wajen yakar shan muggan kwayoyi, domin suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen samar da hukunci mai tsauri daidai da laifukan shan muggan kwayoyi.
Ta yi kira ga ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati da kuma kungiyoyin addini, cibiyoyin ilmi da iyaye da su hada kai da gwamnati a yaki matsalar.
A cewar Dokta Adagwu, ya kamata kuma gwamnati ta sauya tunanita daga yadda take kallon matsalar daga mahangar shari’ar ta kalle shi ta fuskar kiwon lafiya.
Shi ma Obot, wanda masanin halayyar dan Adam ne, ya ce matsalar ta fi batun laifi, saboda tana da tasiri ga lafiya da zamantakewar jama’a, tare da haddasa tashin-tashina da sauransu matsaloli a cikin al’umma.
Ya ce babu wani rukuni ko jinsi na al’umma da ba ya amfani da kwayoyi, bambancin kawai shi ne irin kwayoyin da suke amfani da shi.
A cewarsa, miyagun kayan sun hada da hodar iblis, tabar heroin, sai kuma abubuwan kara kuzari da wadanda ake shaka da sinadarai masu narkewa kamar gam.
Ta ke kira gare su, Farfesa Adeyeye ta shawarci matasa da su guji shan miyagun kwayoyi domin hakan na haifar da hadari har ma da mutuwa.
“Muna bukatar tsamo matasanmu daga amfani da haramtattun kwayoyi, don cimma wannan, dole ne duk wadanda lamarin ya shafa hukumomin da abin ya shafa su hada kai,” inji ta.
Sagir Kano Saleh daga Julius Enehikhuere, NAN.