An ceto ‘yan mata ’yan Najeriya su 71 da aka yi safararsu zuwa Lebanon wadanda aka gani a wani hoton bidiyo suna rokon a cece su.
Da sanyin safiyar Litinin ne dai ’yan matan suka sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Shugaban reshen Abuja na Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA), Mista Bitrus Samuel, ya shaida wa Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya (NAN) cewa wannan ne ayari na biyu na ‘yan mata ‘’yan Najeriya 150 da aka yi safararsu zuwa kasar ta Lebanon.
- ’Yar Najeriya da aka sayar a matsayin baiwa ta dawo gida
- Wahalar da mata ’yan Najeriya ke sha a Saudiyya
Idan ba a manta ba, a farkon wannan watan ne dai ayari na farko da ya kunshi na ’yan mata 94 ya sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Mista Samuel ya ce daga filin jirgin wadanda aka ceto din za su wuce otal, inda Hukumar Hana Safarar Mutane ta Kasa {NAPTIP) za ta dauki bayanansu.
Hukumar za kuma ta killace su don gudun yaduwar cutar COVID-19.
Shi ma kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Mista Ferdinand Nwonye, ya ce ceton ’yan matan ya biyo bayan bazuwar bidiyon da suka yi ne suna kira ga gwamnatin tarayya da sauran ’yan Najeriya su kai musu dauki a intanet.
Ya kuma ce sai da ma’aikatar ta tattauna a lokuta da dama da jakadanta a Najeiya, Mista Houssam Diab, kafun gwamnatin Lebanon ta yarda ta sako ’yan matan.
Jami’an gwamnati daga hukumar NAPTIP da Ma’aikatar Harkokin Waje, da kuma Hukumar Kula da ’Yan Najeriya da ke Kasashen Waje (NIDCOM) ne suka tarbi ’yan matan.