Ranar Talatar makon da ya gabata ne 05-08-14, Kwamitin nanmai mutane bakwai da Babban Cif Jojin jihar Nassarawa maishari`a Sulaiman Dikko ya kafa a bisa ga kudurin da Majalisar Dokokin jihar ta zartar, don ya binciki zarge-zargen aikata ba daidai ba da Majalisar ta yi wa gwamnan jihar, Alhaji Umaru Tanko Al-Mukura a karkashin jagorancin Lauya Yusuf Shehu Usman ya sa soso da sabulu ya wanke gwamnan na babbar jam`iyyar adawa ta APC, akan ya aikata zarge-zargen 16, da Majalisar Dokokin jihar ta ke zarginsa da aikatawa. Zarge-zargen dasuka kama daga yin almubazzaranci da sama da fadi da dukiyoyin al`ummar jihar da yin nade-nade da wai suka saba wa tande-tanaden kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999, kamar yadda akai masa kwaskwarima.
Wankewar da Kwamitin ya yi wa gwamnan jihar ta Nassarawako kusa ba ta zo ma masu kula da al`amurran da ka je su dawo ba a harkokin yau da kullum da mamaki ba, musamman na jiharta Nassarawa, bisa ga irin yadda wasu `yan asalin jihar manya dakanana a lungu da sako na jihar da ma na kasa baki daya sukarinka nuna adawarsu da wancan yunkuri. Alal misali dauki irinyadda tun a ranar 14-07-14, da `yan Majalisar Dokokin jihar na PDP suka zartar da kudurin tsige gwamnan, zama ya gagare sua mazabunsu da shi kansa babban birnin jihar, bare kuma a cikin zauran Majalisar da ke Babban jihar.
Hatta zaman da `yan Majalisar suka yi inda suka barranta Majaisar Dokokin jihar daga Kwamitin binciken na mutane bakwai din, inda suka yi zargin wai wasu daga `yan Kwamitin ko dai abokan gwamnan jihar ne, ko kuma `yan siyasa ne, har suka kuma nemi lallai sai Babban Jojin da ya gaggauta rushe Kwamitin ya kafa wani da zai kunshi nagartattun mutane kuma`yan baruwanmu, ba a garin Lafiya suka yi shi ba, a garin Karu da ke kan iyakar jihar da babban birnin tarayya Abuja suka yi shi a wani Otel. Dadin-dadawa kuma ga shi duk da hutun zaman Majalisar (wanda suke cikinsa ne suka dawo suka yi zaman na musamman don tabbatar da tsige gwamnan jihar) da `yan Majalisar suka yi ya kare, ya kuma kamata su dawo bakin aiki tunranar Litinin din makon jiya 04-08-14, amma fargabar abin da ka iya faruwa akan su in sun koma ya sanya suka ki komawa zamannasu a ranar, suna can suna ta labe-labe.
Kazalika, yunkurin tsige gwamnan ya tunzura mutanen jiharhar suka fara zanga-zanga a garin Karu da babban birnin jihar da wasu garuruwan jihar irin su Akwangwa da makamantansu, zanga-zangar da har ta yi sanadiyar mutuwar mutane biyu, ko ba komai ya tabbatarwa da mai karatu cewa Gwamna Al-Makura yana zaune lami lafiya da mutanensa, koda kuwa gwamnatinsa ta rinka sawa ana zanga-zangar, don ai masu iya magana kan ce “Gudu samun dama tsayuwa samun dama.”
Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da ita kanta jam`iyyarsa ta PDP, sun shiga cikin batun neman lallai sai `yan Majalisar su janye aniyarsu ta tsige Gwamna Al-Makura, ta hanyar wani taro da suka yi da wasu daga cikin shugabannin `yan Majalisar Dokokin Jihar Nassarwa a karkashi shugabancin Kakakinta Alhaji Musa Ahmed Mohammed a fadar gwamnatin tarayya a lokacin da ake tsakiyar danbarwa tsigewar, amma ka iya cewa wancan taro bai yi wani tasiri ba, saboda bayan taron ne, shugabannin jam`iyyar PDP reshen jihar suka yi wani taro da manema labarai a Lafiya, inda suka ce ba gudu ba ja da baya akan wancan yunkuri na tsige gwamnan. Don haka ba mamaki shugaban kasa ya shirya taron ne kawai bisa ga irin ca… din da aka yi masa da jam`iyyarsu akan sun dukufa wajen ganin sannu a hankali za su tsige gwamnonin jam`iyyar adawa ta APC, bayan tsige gwamnan APC na jihar Adamawa Alhaji Murtala Nyako, a `yan kwanakin nan, da irin yadda suka dukafa cikin halin ko ana ha maza, ha mata, sai sun ci zaben gwamnnan jihar Osun, wanda ya yanzu ta tabbata jam`iyyar APC ta kare kambinta a sakamakon lashe zaben karshen makon da ya gabata.
Yanzu wasu daga cikin abubuwan da aka zuba wa idanu a gania cikin siyasar jihar, bayan yunkurin tsge gwamnan ya ci tura, shi ne ta ina kuma Majalisar Dokokin jihar da ita kanta PDP, za su bullo wa batun idan har ba su amince da rahoton Kwamitin binciken ba, da ya ce bai samu gwamnan da aikata wani laifi ba.
An dai ruwaito shugaban Kwamitin yada labarai, kuma Kakakin Majalisar Alhaji Mohammed Baba Ibakutun kafin Kwamitin bincike ya fara zamansa da bayan ya fara zama ya dage akan cewa, Majalisar Dokokin ba ruwanta da zaman Kwamitin bare rahotonsa, ko kuwa koda Lauyoyin da Majalisar ta tura a zaman Kwamitin binciken cewa sukai sun barranta da Kwamiti da rahoton da zai bayar.
Yanzu kuma bayan kammala zaman kwamitin an sake jin Alhaji Ibaku, yana cewa Kwamitin ba shi da iko ko hurumin da zai ce ya kori zarge-zarge, ya ce kamata ya yi Kwamitin ya rubuta tare da mika wa Majalisar rahotansa. Kai ka ji mai karatu, wannan shi ne, ba cinya ba kafar baya, Majalisar da tun farko ta barranta kanta da kwamitin da aikinsa, me kuma daga baya za ta yi da aikinsa? Ba kome ya kawo haka ba, mai karatu sai bisa ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar nan, yanzu Majalisar Dokokin ko wata kotu a kasar nan ba abin da za su iya yi akan batun a tsige gwamnan wato magana ta wuce ke nan har abada na bada.
Da wannan fage da aka kai a jihar, ina ga ya kamata bangaren gwamna (masu zartarwa) da na Majalisar Dokoki da na sharia`a su hada karfi da karfe waje daya, don ganin sun ci gaba da yi wa mutanen jihar ayyukan da za su kyautata rayuwarsu. Yanzu dai sun ga irin yadda yunkurisu ya kare kuma koda wani za su sake yi don suna takama da suna da gwamnatin tarayya da kuma rinjaye `yan Majalisa 20, daga cikin 24, APC, mai gwamnatin jihar na da 4, rak, wadda aka kwata yanzu ita za a sake kwatawa, don mutanen jihar manya da kanana sun nuna suna zaune lafiya da gwamnansu, don haka ya kamata su kwan da sanin in sun san wata, ba su san wata ba. Kokowar shekarar 2015, su fauwala wa Allah.
’Yan Majalisar Nasarawa ba su san dawon garin ba
Ranar Talatar makon da ya gabata ne 05-08-14, Kwamitin nanmai mutane bakwai da Babban Cif Jojin jihar Nassarawa maishari`a Sulaiman Dikko ya kafa a bisa…