’Yan bindiga sun saki ’yan Kasuwar Kantin Kwari da ke Jihar Kano da aka yi garkuwa da su a Jihar Kogi a kan hanyarsu ta zuwa fatauci a garin Aba, Jihar Abiya.
Majiyarmu ta ambato Shugaban Kungiyar Matasan ’Yan Kasuwan Arewa na Najeriya, Alhaji Abubakar Babawo, na cewa an sako ’yan kasuwar na Kantin Kwari ne a yammacin ranar Asabar bayan sun shafe kwanaki a hannun masu garkuwar.
- Tsoron iyayenmu na hana maza neman aurenmu —’Yan matan barikin soja
- An kama kwarto ya haka ramin da ke kai shi gidan auren tsohuwar budurwarsa
- Mata dubu: An daure mai wa’azi shekara dubu
- Buratai ya jinjina wa sojoji kan murkushe Boko Haram a Marte
“’Yan kasuwar Kano… na daga cikin mutum 27 da suka kubuta daga hannun ’yan bindiga a ranar Asabar da yamma.
“Muna ta magana da su, sun kwana a Kaduna, yau (Lahadi) ake sa ran isowarsu Kano”, inji shi.
Ya ce dukkanin ’yan kasuwar da aka yi garkuwa da su din ne aka sako bayan an biya kudin fansa, sai dai bai bayyana ko nawa ne ba.
A ranar Lahadin da ta gabata ce ’yan bindiga suka tare motar ’yan kasuwar a kan hanyar Lokoja-Okene suka tisa keyarsu zuwa cikin jeji a garin Okene.
Manajan-Daraktan Hukumar Gudanarwar Kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Abba Bello ya tabbatar mata cewa, “Suna hayarsu ta zuwa fatauci a garin Aba na Jihar Abiya ne ’yan bindiga suka tare motarsu a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Okene a Jihar Kogi.
“Mutane na cewa wadanda aka yi garkuwa da su za su kai mutum 20 ko fiye da hakan, amma adadin da muka iya tabbatarwa shi ne mutum 18,” inji Alhaji Bello a wancan lokacin.
Ya zuwa yanzu, Aminiya na kokarin tuntubar iyalan ’yan kasuwar da hukumomin Kasuwar Kantin Kwari domin kawo muku karin bayani a a nan gaba.
Kananan ’yan kasuwa da dama a Kasuwar Kantin Kwari kan yi tafiya a motoci zuwa garin Aba, cibiyar kasuwancin Jihar Abiya, domin su sayo yadi ‘Dan Aba.’