✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwan Kwari sun bukaci gwamnatin ta shiga tsakaninsu da Kwastam

kungiyar ‘Yan Kasuwar Kantin Kwari a Jihar Kano sun nemi Gwamnatin Tarayya da ta sa baki wajen ganin ta karbo musu kayayyakin sutura da suke…

kungiyar ‘Yan Kasuwar Kantin Kwari a Jihar Kano sun nemi Gwamnatin Tarayya da ta sa baki wajen ganin ta karbo musu kayayyakin sutura da suke sayarwa na biliiyoyin Naira da Hukumar Hana Fasa kwari ta kasa (Kwastam) ta kwace.

A makonni baya ne Hukumar ta Kwastam ta garkame sito-sito ajiye kaya na ‘yan kasuwar Kwari, inda ta bayyana cewa an shigo da su ta hanyar da ba ta dace ba.
Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar yan kasuwar Alhaji Nura Idris Maliya ya bayyana wa Aminiya cewa wannan kaya da hukumar ta kwastam ta kama ba wai mallakar ‘yan China ba ne, hadin gwiwa ne tsakanin wasu ‘yan kasuwar Kano da mutanen China. “Mun dade muna gudanar da wanann
harka ta kasuwanci a tsakaninmu da ‘yan kasar China, inda suke shigo mana da kaya muna sayarwa a kasuwarmu. Muna kuma biyan duk wani kudi na shigo da kaya kasar nan. Kwatsam sai ga shi mun wayi gari an kama mana kaya”
Da yake bayyana irin asarar da kame kayan ’yan kasuwar da Kwastam ta yi ya haifar, Alhaji Nura Maliya ya ce: “Baya ga fama da rashin kaya da muke fuskanta a kasuwa, kasancewar mu muke bai wa dukkanin jihohin yankin Arewa da makwabtanmu na wasu kasashen kaya, to yanzu haka babu kaya a kasuwa. Haka kuma wadanda a yanzu suka rage a hannunm farashinsu ya yi tashin gwaron zabi,” inji shi.
Alhaji Maliya ya yi nuni da irin illar da korar ‘yan kasuwar kasar China daga kasuwar tasu za ta iya haifarwa, inda ya ce hakan ba karamin nakasu zai haifar ga kasuwar da kuma jihar gaba daya ba.
Idan ba mu manta ba a lokutan baya da aka yi gyada tunda aka kori Turawa shi ke nan harkar ta mutu. Haka kuma lokacin da aka yi harkar fatu. “Don haka a yanzu ba ma fatan a sake maimaita irin hakan,”inji shi.
A cewar Alhaji Maliya suna tunanin watakila ’yan kasuwar wasu jihohin ne suka yi wa Jihar Kano cinne don ganin an lalata lamarin kasuwanci a jihar. “Muna tunanin wasu ne ke bayan shirya mana wannan badakala, don ganin an murkushe harkar kasuwanci a jihar, ganin cewa tun farkon
zuwan ‘yan China Kano wasu ’yan kasuwa daga jihohin Kudanmcin kasar nan suka yi ta kokarin sai yan Chinan sun koma garuruwansu, amma su kuma suka ki, sai suka nuna cewa sun fi sha’awar zama a Kano don gudanar da kasuwancinsu,” inji shi.
Alhaji Maliya ya yi kira ga gwamnatin da ta yi kokarin gyara harkar wutar lantarki da samar da tsaro a kasar nan ta yadda za a samu masakun kasar nan su farfado tare da samar da yawan kayan da ‘yan Najeriyar ke bukata.
Daga karshe ya ce: “Ya kamata gwamnati ta duba da cewa lokacin Sallah yana karatowa, don haka jama’a suna bukatar kaya sosai. Haka kuma akwai bukatar gwamnati ta inganta wutar lantarki don ganin masakunmu sun farfado.”