✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan giya uku

Wasu mutane ne su uku suka sha giya suka yi tatil, sun fito daga gidan giyar sai suka tsayar da dan tasi; suka ce ya…

Wasu mutane ne su uku suka sha giya suka yi tatil, sun fito daga gidan giyar sai suka tsayar da dan tasi; suka ce ya kai su unguwarsu. Da ya fahimci cewa a buge suke, bayan sun shiga sai ya taka totur da karfi, ya ba motar wuta, bai matsa ko’ina ba, sai ya sauko ya bude motar, ya ce musu: “Ku sauko, mun zo inda za ku sauka.” Na farko ya fito sai ya biya kudin motarsu duka. Na biyu ya yi godiya, shi kuma na uku sai ya falla wa dan tasi mari. Direba ya tambayi dalilin mari sai ya ce masa: “Ka yi tukin ganganci, ka kusa kashe mu, shi ya sa na mare ka!”
Daga Zee Man Fagge, Kano 08034412272