Wasu mutum biyu ’yan gida daya sun rasu bayan tashin gobara a gidansu da ke unguwar Sheka a birnin Kano.
Hukumar Kashe Gobarar ta Jihar Kano ta ce wutar ta tashi ne bayan bude baki ranar Juma’a, a wani bene da ke daura da titin Gidan Zoo.
- Sai da na daina bara na samu arziki —Nakasasshe
- Ban iya turanci ba —Adam Zango
- Harin ’Yan bindiga: Saudiyya ta ba da tallafin abincin $1.2m a Zamfara
Kakakin Hukumar, Saminu Abdullahi, “Benen mai dakuna hudu da falo biyu ya kone kurmus a gobarar.
“Mun samu kiran neman dauki daga wani mutum mai suna Sabo Wada da misalin karfe 10.10 na dare cewa gobara ta tashi a wani gida a unguwarsu, inda mutum uku suka makale, ciki har da karamar yarinya mai shekara hudu.
“Nan take muka tura jami’anmu domin aikin ceto, inda suka isa wurin da misalin 10.15 na dare.
“An ceto mutum biyu daga cikinsu a halin rai kwakwai, mutu kwakwai, aka garzaya da su Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, inda likitoci suka tabbatar cewa sun rasu.”
Sanarwar ta ce mai gidan da ’yarsa mai shekara hudu sun kubuta, amma mai dakinsa da kanwarsa da ke gidan sun rasu a gobarar.
Sai dai a bayanin da ta fitar a safiyar Asabar, Hukumar ta ce ba a kai ga gano musabbabin gobarar ba tukuna.