Akalla mutum 800 a kasar Uganda ne ’yan damfara suka dura wa ruwa a maimakon rigakafin COVID-19 a cikin watan Yuni.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ma’aikata ke rige-rigen karbar rigakafin kamar yadda hukumomin kasar suka bukata don takaita ci gaba da yaduwar cutar a kasar.
- COVID-19: China ta tallafa wa Najeriya da rigakafi 470,000
- Harin ’yan bindiga ya jikkata ’yan sanda uku a Kaduna
Wasu kamfanonin har biyan kudi suke yi saboda a yi wa ma’aikatansu rigakafin a wuraren aikin nasu, amma daga bisani hukumomi suka gano ’yan damfara ne kawai suke dura wa mutane ruwa a maimakon rigakafin, kamar yadda Warren Naamara, Darakta a Ma’aikatar Lafiyar Kasar ya tabbatar.
Tuni dai Daraktan ya tabbatar da kama mutum biyu bisa zargin aikata ta’asar.
Kasar Uganda, wacce ke yankin Gabashin Afirka na fama da zagaye na biyu na annobar ta COVID-19 wacce sabuwar nau’in da ake kira da ‘Delta’ ta kara ta’azzarawa.
Adadin wadanda suka kamu da ita ya zuwa karshen watan Mayu ya kai kimanin 91,162, a maimakon 47,147 din da suka kamu a karshen watan Mayu, inji Ma’aikatar Lafiyar kasar.
Mutane miliyan daya da dubu dari da sha hudu ne dai aka yi wa rigakafi nau’in AstraZeneca a kasar wacce ke da mutane miliyan 42.7, ta hanyar tallafin da gwamnatin kasar Indiya ta bata.
Ana sa ran nan da karshen watan Yuli kasar za ta karbi karin rigakafi 285,600, sai kuma karin 687,800 a watan Agusta, kari a kan guda 300,000 da kamfanin Sinovac ya bata a watan Yuli.