✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan daba sun sace sandar girman Sarkin Legas

’Yan daba sun yi wa fadar Sarkin Legas da ke unguwar Iga Idugaran, kawanya suka yi farfasa motoci da kayayyakin tarihi. Wani bidiyo da ke yawo a…

’Yan daba sun yi wa fadar Sarkin Legas da ke unguwar Iga Idugaran, kawanya suka yi farfasa motoci da kayayyakin tarihi.

Wani bidiyo da ke yawo a shafukan zumunta ya nuna gungun ’yan daba na gudu a kan titi da sadar girman sarkin da ake kira “Opa Ase”.

Wani mazauni Legas ya tabbatar da cewar, ’yan dabar da suka sace sandar girman Oban ne suka kona gidan iyayen Gwamna Babajide Sanwo-Olu.

“Da suka kai farmaki gidan iyayen Gwamna Sanwo-Olu, ’yan sanda sun harbi wasu daga cikinsu.

“Hakan ya harzuka su suka yi musayar wuta har suka ci karfin ’yan sandan da ke karkashin ofishin Adeniji Adele suka tsere.

“Daga nan sai gungun ’yan dabar suka shiga fadar Sarkin Legas (Oba) suka yi fashe-fashe.

“Matasan sun ce suna lalata kayan gwamnati ne kuma sarkin yana cikin gwamnati”, kamar yadda ya sanar da jaridar Punch.