✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan daba sun kone mutum-mutumin Azikiwe

’Yan daba sun kone gunkin Shugaban Kasar Najeriya na farko, Nnamdi Azikiwe, a Onitsha, Jihar Anambra

’Yan daba sun kone gunkin Shugaban Kasar Najeriya na farko, Nnamdi Azikiwe, a garin Onitsha, Jihar Anambra.

’Yan dabar, sun je farfajiyar da aka dasa gunkin ne dauke da muggan makamai suka rika farfasa shi, daga bisani suka banka masa wuta.

“Kai ka jefa mu cikin wannan matsalar” na daga cikin kausasan kalaman da ’yan dabar suka rika jifar gundin Zik din da su.

Gwamnan jihar, Willie Obiano, ne ya gina gunkin a shataletalen DMGS, da ke Onitsha domin kawata garin.

Mista Victor Ononye, dan uwan Azikiwe na jini, ya yi tir da abin da matasan suka yi.

Ya ce, Azikiwe, a matsayinsa na wanda ya nema wa Najeriya ’yancin kai, dole ya yi fushi da abin da suka yi.

“Abin da ya faru a shataletalen DMGS a Onitsha da ido na ya game mani, ya saka ni hawaye”, inji shi.

Ononye da ya la’anci ’yan dabar da suka rataya wa gunkin Zik din tayoyi kafin suka banka masa wuta.

“Sai da suka guntile masa hannaye kafin su tafi da sarkar girman da aka rataya masa.

“Wannan rashin godiya da jahilai wadanda ba su san komi ba kan tarihi ne ba za su yi,” inji shi.

Ononye ya ce, yan dabar sun lalata duk wata kwaliua da aka yi domin kawata farfajiyar da aka dasa gunkin.

“Basu da yawa, amma ’yan sanda da ke tsaye kusa da inda abin ya faru ba su dauki mataki ba.

Ya ce matasan duk sun balle karafan da aka zagaye farfajiya da aka dasa gunkin, sun kuma farfasa kwayayen lantarkin da aka haskaka wurin da su.

“Na ga ‘yan banga biyu, dauke da bindiga sun zo gurin bisa mashin, amma sai suka wuce bayan matasan sun yi musu kirari.

“Abin tausayi ne! Zik na Afirka da ya kawo karshen yakin basasa, wanda ya gina daya daga cikin jami’oin farko da ta yi zarra a fagen ilimi, bai kamata a yi masa haka ba”, inji shi.