✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Boko Haram sun kashe mutum 20 a wajen jana’iza a Yobe

Sun kashe mutanen ne ta hanyar dasa musu bam suna tsaka da jana’iza

Wasu mahara da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kashe mutum 20 a kauyen Nguro Kayayya da ke Karamar Hukumar Geidam a Jihar Yobe, lokacin da suke tsaka da jana’izar mutum 16 aka kashe musu.

Tun da farko dai maharan a kan babura sun halaka mutum 16 tare da kona wasu da ransu da kuma jikkata wasu da dama a kauyen.

Sai dai ’yan ta’adda sun sake komawa a yayin da ake tsaka da jana’izar mutanen da suka kashe inda suka tayar da wasu abubuwan fashewa da suka kashe karin mutum 20.

Wata majiya a yankin ta shaida wa Aminiya cewar har yanzu akwai wasu karin mutanen da ba a gan su ba.

Wata majiya da yammacin Laraba ta shaida wa wakilinmu cewa ’yan ta’addan sun fara kai hari kauyen ne da misalin karfe 10:00 na daren Litinin.

Sai dai ana tsaka da jana’izar wadancan mamatan a ranar Talata sai ’yan ta’addan sun sake kimawa kamar yadda aka ambata a baya, inda suka kara kashe mutane ta hanyar amfani da bam.

Akalla mutane 20 ne suka mutu, tare da jikkata wasu da dama a wannan hari na biyu.

A cewar majiyar, ’yan ta’addan sun koma garin ne ranar Talata, inda suka dasa bam a kan hanyar da ta kai ga makabartar tare da afkawa mutanen da suka halarci jana’izar.

“Abin takaici, mutane 20 ne suka sake rasa rayukansu a lokacin da bam din ya tashi a hanyarsu ta dawowa daga makabarta,” kamar yadda wata majiya ta shaida wa wakilinmu.

A cewar majiyar  bayan shafe sa’o’i da dama ’yan ta’addan na cin karensu ba babbaka a cikin wannan kauyen, sun kuma koma wani kauyen da ke makwabtaka da su mai suna Joro, inda suka kona shi gaba daya.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga jami’an jihar har ya zuwa lokacin da aka fitar da rahoton a kan harin.