✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindigar Sakkwato da Zamfara ne ke addabar Neja — Sanata

Sanatan ya bukaci jami'an tsaro da su kara zage damtse wajen yakar 'yan bindiga a jihar.

Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta Arewa a Majalisar Dattijai, Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce ’yan bindigar da sojoji suka fatattaka daga jihohin Sakkwato, Zamfara da Katsina ne suke addabar jihar Neja.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake gabatar da kudiri a gaban majalisar kan matsalar ’yan bindiga da jihar ke fuskanta.

  1. Buhari na neman majalisa ta amince da sabon shugaban Sojin Kasa
  2. ‘Shan sigari kan hallaka ’yan Najeriya 29,472 a kowacce shekara’

Dan majalisar ya ce Kananan Hukumomi biyar a mazabarsa na fama da hare-haren ’yan bindiga ba dare ba rana.

Ya ce tsakanin yammacin Litinin zuwa safiyar Talata kawai, an kashe mutane takwas tare da jikkata wasu da dama a hare-haren da aka kai wa wasu al’ummomin da ke kan hanyar Tegina zuwa Kwantagora a jihar.

A cewarsa, hare-haren sun tilasta wa sama da mutane 50,000 yin kaura daga muhallansu tare da neman mafaka a sansanin ’yan gudun hijira da ke jihar.

Akan haka sai ya bukaci jami’an tsaro da su kara kaimi wajen yakar ’yan ta’adda a jihar Neja da ma sauran jihohi da ke fuskantar kalubalen tsaro daga ’yan bindigar.